Gwamnatin jihar kano ta umarci masu gudanar da sana’ar gwangwan dake jihar kano da su dakatar da sayo kayayyakin gwangwan daga yankin Arewa maso Gabas na ƙasar nan sakamakon iftila’in da aka samu a jihar nan a kwanan nan kan yadda aka samu abubuwan fashewa a jihar sanadiyyar kayan gwangwan da suke da alaƙa da yankin Arewa maso gabas ɗin ƙasar nan.
Kwamishinan tsaro na jihar kano AVM Ibrahim Umaru mai ritaya ne ya bayyana hakan a yau yayin wata ganawa da ƙungiyar masu sana’ar gwangwan na ƙasa reshen Arewa kan irin iftila’in da ya fara a jihar Kano a lokutan nan sanadiyyar kayan gwangwan.
Avm Ibrahim Umaru ya ƙara da cewa an ɗauki wannan matakin ne domin kare rayukan da dukiyoyin al’ummar jihar Kano.
Da yake jawabi shugaban ƙungiyar masu sayar da kayan gwangwan na yankin Arewa Alhaji Aminu Hassan yace sun gamsu da wannan umarnin da gwamnatin kano ta bayar na dakatar da shigo da kayan gwangwan daga yankin Arewa maso Gabas domin kare jihar kano daga barazanar tsaro.
Wakilin mu ya rawaito cewa Kwamishinan ya kuma gargadi ƙungiyar da su kasance masu bin umarnin da aka basu domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma