Babbar Kotun Tarayya me lamba 1 dake Gyadi gyadi Court Road Karkashin me Shari’a SM Shu’aibu ta yi umarni ga Hukumar EFCC data cigaba da bincike kan filin Musabaka da ake zargin wasu Jagororin Musabaka a Jihar Kano sun siyar ba bisa ka’ida ba
Asali dai tsohon Gwamnan Jihar Kano Marigayi Abdullahi Wase ne ya bayar da filin ga ‘Yan Musabaka a shekarar 1995 a yankin Ahmad Bello dake Nassarawa GRA dan gina Cibiyar Musabaka, hakan yasa wasu daga cikin masu musabakar su kayi korafi a gaban hukumar EFCC data yi bincike kan lamarin, haka tasa ‘Yan Kwamitin suka garzaya gaban Kotu dan ta dakatar da EFCC daga bincikar su.
Sai a hukuncin da Kotun ta gudanar a yau juma’a ta umarci hukumar EFCC ta cigaba da binciken tare da bawa wadanda ake kara da hukumar EFCC Naira 250,000 sakamakon bata musu lokaci a gaban kotun.
Bayan fitowa daga kotun wakilinmu ya zanta da lauyan wadanda akai kara wato Barista Salihu Abubakar
ya ce kudin filin da akai zargin Jagororin musabakar sun siyar ya kai 4.5bn, yana me cewa dama fatan su adalci sun kuma gamsu da hukuncin na yau.
Lauyan da yake kare Malaman da suke gudanar da Musabaka Barr Yahaya Isa Abdurrashed ya ce abinda suke kalubalanta a gaban. kotu shi ne ba hurumin EFCC ba ne tun da yana gaban Kotu, amma duba da hukuncin na yau sun nemi a ba su copy domin yin nazari, za kuma su daukaka kara.