Gwamnatin jihar Kano ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan dari da hamsin da Daya don sake gina masallacin da wani matashi ya kona masallata a garin Tiga Gadan dake karamar hukumar Gezawa a ranar 16 ga watan Mayun shekarar data gabata ta 2024. Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da alamuran cikin gida na jihar Kano Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar.
Sanarwar ta kuma ce, ginin zai hadar da na Islamiyya da Ofisoshi da kuma gyaran bandakuna tare da samar da wutar Sola da kuma fanfan tuka-tuka.
Gyaran masallacin na daga cikin alkawarin da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi wa alummar garin na Gadan lokacin da ya kai ziyara na cewar zai gudanar da gyaransa.
Kazalika ta cikin sanarwar gwamnan ya bukaci al’ummar yankin na Gadan da su bayar da hadinkan da ya kamata wajen tabbatar da aikin tare da kula da su idan an kammala.