Gamayyar kungiyar tsaffin daliban makarantan Abdullahi Mai masallacin dake Unguwar Gini cikin karamar hukumar Birnin Kano ta ce zata cigaba da samar da kayan koyo da koyarwa dan tallafawa dalibai masu tasowa da Bunkasa Ilimi.
Shugaban kungiyar Nura Yusif,ne ya bayana haka jiya Lahadi lokacin da yake kadamar da dakin gwaje-gwajen da kungiyar ta daga darajarsa tare da samar da kayan aiki na zamani a makarantar Abdullahi Mai Masallaci dake Unguwar Gini a nan Kano.
Nura Yusif, ya Kuma Kara da cewar sun tara kudaden da suka tallafawa makarantar ne daga mambobinsu da Kuma daidaikun mutanen tare da kashe fiye da naira Miliyan daya da dubu Dari uku wajen inganta hanyoyin da makarantar zata kara samun kudin shiga.
A nasa Jawabin Shugaban makaranta Abdullahi Mai masallaci Malam Abubakar Ibrahim, cewa yayi samar da dakin gwaje-gwajen abune da ake kan bukatarsa kuma zasu tabbatar da dalibai sun yi amfani da shi yadda ya kamata.
Da yake nasa Jawabin shugaban kungiyar iyaye da Malamai na makarantar Sheik Tijjani Mai salati, wanda Isah Shehu Ringim ya wakilta, ya godewa kungiyar tsaffin daliban tare da kira ga hukumar makarantar wajen yin amfani da kayan da aka samar yadda ya kamata dan bunkasa Ilimi”