Ma’aikatar mata da Kananan Yara da kuma masu bukata ta musamman taci alwashin hada hannu da ma’aikatar Ilimi ta jihar dan kawo karshen cin zarafin kananan yara a makarantu.
Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata Hajiya Amina Adullahi Sani HOD, da ta samu wakilicin Daraktan Mulki da gudanarwa na ma’aikatar, Muhammad Sambo Iliyasu, ce ta bayyana hakan yayin bikin ranar yara ta Duniya da ya gudana a dakin taro na gidan gwamnatin Kano a jiya Talata.
Itama shugabar gudauniyar EL’S Foundation tace zasu dauki nauyin wasu daga cikin yaran da suka nuna kwazo a wajen taron dan tallafa musu.
Wakilinmu SSM ya rawaito cewa kungiyoyin fararen hula daban-daban ne suka halarci bikin tare da raba kyaututtuka ga yara.