Mai martaba Sarkin Kano Khalifah Muhammadu Sunusi Na Biyu,ya ce Sai Iyaye da sauran Alumma sun Koma bin koyarwar Addini da kuma Inganta tarbiya matukar ana son fita daga halin gubacewar marasa da ake fuskanta fadin jihar Kano da Kasa Baki daya.
Sarkin ya bayana hakan lokacin saukar karatun Alkur’ani Mai girma na dalibai Saba’in Karo na takwas da ya gudana Jiya Lahadi a makarantar Ma’ahad Abdulhamid littahfezil Kur’an dake Unguwar Shatsari cikin karamar hukumar dala a nan Kano.
Mai martaba Sarkin na Kano Wanda Jarman Kano Alhaji Ahmad Umar, ya wakilta ya Kara da cewar Kula da tarbiya da Kuma Ilimin adidini abune da kowa ya kamata ya Kula da shi dan ceto matsa daga halin da suke shiga.
A nasa Jawabin shugaban makarantar ta Ma’ahad Abdulhamid littahfezil Kur’an cewa yayi makarantar ta shafe fiye da shekaru hamsin Wanda har yanzu tana da kalubale.
Wasu cikin daliban da suka sauke Alkur’ani Mai girma sun bayana godiyarsu Ga Iyaye da Kuma Malaman su.
Taron saukar ya samu halartar Malamai da dama Wanda sukayi Jan hankali ga matasa wajen Neman Ilimi da Sana’a dan kaucewa fadawarsu Daba ko taammali da miyagun kwayoyi.