Karamar hukumar Rano ta bukaci al’ummar garin da su kwantar da hankalin su tare da bin Doka da oda Inda zata ci gaba da bin kadin hatsaniyar da ta faru a baya bayan nan da ya haddasa rasuwar Baturen ‘yan sandan Yankin wato DPO, da wani matashi Bakanike.
Shugaban karamar hukumar Hon Muhammad Nazir Ya’u ,ne ya bukaci hakan a yammacin yau a wani taron manema Labarai da ya gudana a sakatariyar ‘yan Jaridu ta jiha NUJ.
Muhammad Naziru Ya’u , ya ce karamar hukumar na aiki tare da Jami’an tsaro da masu Ruwa da Tsaki a Fannonin Rayuwa daban -daban, don ganin an yi bincike tare da tabbatar da gaskiya da Adalci, da ya bukaci Al’umma su koma harkokin su na yau da kullum.
Shugaban ya yi kira ga iyaye da su Kula da tarbiyyar yaran su , a hannu daya kuma ya bukaci matasa da su guji daukar Doka a hannun su , Wacce daga karshe ka iya haddasa da na Sani.