Babbar kotun shariar musulunci ta Rijiyar zaki wadda ke zamanta a Danbare ta yankewa matashin nan wato Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe wasu mutane yayin da suke gudanar da sallar Asuba a garin gadan dake karamar hukumar Gezawa.
Lauyan gwamnati Barista Salisu Muhammad Tahir ya gabatar da lauyoyin dake mara masa baya wato Barista Yusura M Hanga da Barista Basiru Aliyu
Itama lauya mai kare wanda ake tuhuma daga ofishin lauyoyin taimako Barista Asiya Imam ta gabatar da kanta.
Mai sharia Halhalatul Kuzai Zakariyya yayi karatun baya yakuma sake karanto tuhume tuhumen kisan Kai da Barna ta hanyar sanya wuta da samar da mumunan rauni mai sharia yakori shaidar da masu gabatar da Kara suka gabatar wato shaidu biyar takuma karbi shaidu biyu da kuma shaida abin nuni.
Tun a shekarar data gabata ake zargin Shafiu Abubakar da laifukan kisan wasu mutane ashirin da uku ta hanyar cinnamusu wuta a garin Gadan lokacin da suke gabatar da sallar Asuba Hakan yai sanadiyyar rasuwarsu kuma tunda aka gurfanar dashi yake amsa Laifukansa.
Bayan samunsa da laifukan kotu ta yankemasa hukuncin Bulala dari Haka kuma kotun taci tararsa da biyan Naira dubu da dari biyar Haka kuma zaa sake yimasa Bulala hamsin.
Sai laifin kisan Kai inda ta yanke masa hukuncin kisan Kai ta hanyar rataya.