Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da aukuwar wani mummunan lamari a ranar 25 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 8:15 na dare a karamar hukumar Rano, inda aka kama wani mai gyaran babur mai suna Abdullahi Musa, ɗan asalin Rano, bisa zargin tuƙin babur cikin haɗari da kuma yiwuwar kasancewa cikin maye, bayan korafe-korafe daga jama’a.
Bayan an tsare shi, sai ya fara nuna alamun rauni, wanda ya sa aka garzaya da shi Asibitin Gwamnati na Rano, inda ya rasu a safiyar ranar 26 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 6:00 na safe yayin da ake kula da lafiyarsa.
Biyo bayan rasuwar tasa, wasu fusatattun matasa suka kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Rano, tare da kone wani sashi na ofishin da motoci guda biyu, suka lalata wasu motoci goma (10), sannan suka jikkata DPO mai kula da ofishin. An garzaya da DPO ɗin zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, inda daga bisani ya rasu yana karɓar kulawa.
Rundunar Yan sandan ta Kuma ce ta kama mutane ashirin da bakwai (27) da ake zargi da hannu a wannan ta’asa. An kwantar da tarzomar, kuma an dawo da zaman lafiya da doka a yankin.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, PhD, ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru, sannan ya kai gaisuwar ta’aziyya ga Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Mohammed Isah Umar (Autan Bawo 19). Ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin lamarin da daukar matakin doka kan duk wanda aka samu da laifi.
Hukumar ‘yan sanda ta Jihar Kano na jajantawa iyalan marigayi DPO, wanda ya rasa rayuwarsa a bakin aiki, tare da roƙon jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannunsu, su kuma bai wa hukuma hadin kai wajen gudanar da bincike cikin kwanciyar hankali.
Hukumar na tabbatar da kudirinta na ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da doka a jihar, tare da neman goyon bayan al’umma a wannan lokaci.