Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya Sanya Hannu Kan Dokoki Hudu da zasu Kafa Sabbin Hukumomi a Jihar .
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce sa hannu kan dokokin zai inganta ayyukan gwamnati da habaka ci gaban al’umma da tattalin arziki.
Ta cikin waata sanarwa da Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Alhamis, ta kara da cewar Hukumomin da aka kafa sun hada da
Hukumar Kare Walwalar Jama’a ta Jihar Kano wato Kano State
Social Protection Agency,
Da Hukumar Kula da Tallace-Tallace na alluna ta Jihar Kano wato- Kano State Signed Advertisement Agency.
Sai Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Bayanai -Kano State Information Technology Development Agency, da Hukumar Bunkasa Kanana da Matsakaitan Harkokin Kasuwanci ta Jihar – Kano State Small and Medium Enterprises Development Agency.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa wannan mataki yana daga cikin burinsa na gina sabuwar Kano mai cike da ci gaba Yana Mai cewa sabbin hukumomin za su taimaka wajen samar da ayyukan yi, jawo hankalin masu zuba jari, da tabbatar da ingantadyar
manufofin gwamnati.
Ya kuma ja kunnen cewa za a dauki matakin doka kan duk wanda ya karya sabbin dokokin da aka kafa, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta tsaya tsayin daka wajen ganin an bi doka da oda.
Wannan sauyi na daga cikin kokarin Gwamna Abba wajen sake fasalin harkokin gwamnati, kara inganta shugabanci, da mayar da Kano cibiyar kirkire-kirkire da ci gaban masana’antu da tattalin arziki.