Hukumar kashe gobara ta jihar Kano dake arewacin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Darakta Alhaji Sani Anas, ta ce ta shawo kan wata gobara da ta tashi a kasuwar kurmi tare da kone shaguna shida a layin masu sayar da wayoyin hannu wato yan Jjagwal.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar ga manema labarai ta kara da cewa hukumar kashe gobarar ta karɓi kiran gaggawa daga DPO na ofishin ‘yan sanda na Jakara a ranar Juma’a, 18 ga Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 1:35 na dare, game da gobara da ta tashi a kasuwar Kurmi, unguwar Jakara ‘yan Jagal.
Jami’an hukumar daga babban ofishin suka halarci gurin da gobarar ta faru, inda suka tarar da wasu shaguna shida sun kama da wuta sosai, yayin da wasu shaguna guda biyar suka samu ɗan ɓarna kaɗan, amma ba su ƙone ba.
Sanarwar ta kara da cewa ma’aikatan hukumar kashe gobarar sun nuna ƙwazon wajen shawo kan gobarar cikin lokaci, tare da hana yaduwar wutar zuwa sauran shaguna a kasuwar.
An kuma tseratar da kayayyaki da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
A baya-bayan nan, a ranar Talata 15 ga Afrilu, 2025, an samu irin wannan gobara a wannan kasuwa. Saboda haka, hukumar zata gudanar da bincike don gano musabbabin gobarar da kuma ɗaukar matakin hana faruwar hakan a gaba.
Rahotannin sun tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko raunuka ba a lokacin gobarar.