Gwamnatin jihar Kano ta zata inganta tare da dawo da cibiyoyin koyar wa matasa dinki da tsohuwar Gwamnatin Dr Rabiu Musa Kwankwaso ta samar akayi watsi da su tsahon shekaru takwas a kananan hukumomin jihar dan samar da ayukanyi ga mata da matasa.
Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayana hakan yayin ziyarar duba aikin titin kilomita biyar da da gyaran asibitin Minjibir da yammacin jiya Litinin.
Gwamna Abba Kabir Yusif, ya kara da cewa ayukan suna cikin alkawaarin da ya dauka lokacin yakin neman zabe kuma kyautata rayuwar matasa na cikin abubuwan da Gwamnatin sa ta bawa mahimmanci.
Abba Kabir Yusif, ya kuma ziyarci babban Asibitin Karamar hukumar ta Minjibir harma yace zasu cigaba da inganta asibitocin da ke duk kananan hukumomin jihar ta hanyar samar da gine-gine da ma’aikatan lafiya kuma tuni suka dauki dalliban da suka tura karo karatu kasashen waje a fannin lafiya tare da turasu Asibitoci a kananan hukumomin jihar Kano Arbaiin da hudu dan inganta harkokin lafiya.
Da yake jawabi shugaban karamar hukumar ta Minjibir Kaftin Jibrin na lado Kunya, cewa yayi karamar hukumar zata cigaba da hada Kai da Gwamnatin jihar wajen kawo ayukan cigaba.
Gwamnan na Kanon ya kuma bukaci dan kwangilar dake aikin titin na kilomita biyar ya gagauta kammalashi cikin inganci dan amfanin mutanen karamar hukumar ta Minjibir.