Gwamnatin jihar Kano ta ce zata raba kujerun zama Fiye da Dubu goma sha shida a makarantun Firamare dan magance zaman Yara a kasa da Inganta harkokin kayo da koyarwa.
Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar inda ake samar da ababan zaman daliban a Unguwar Gandun Albasa da yammacin Jiya Lahadi.
Abba Kabir ya kara da cewar “samar da kujerun zaman dalibain da aka shafe watanni takwas ana hadasu ya samo asali ne daga Dokar ta baci da gwamnatinsa ta sa a fannin Ilimi don Ingantashi”
Gwamna ya kuma ce “Gwamnati zata sa Ido dan tabbatar da makarantun da dalibai sun amfana Kamar yadda aka tsara tare da bibiyar makarantun da zasu amfana”
A nasa jawabin kwamishinan Ilimi na Jihar Kano Malam Ali Haruna Makoda, ya ce “yanzu haka an kammala mafi yawan kujerun zaman daliban tare da cigaba da hada wasu dan wadata makarantun Firamaren jihar Kano”.
Da yake nasa jawabin shugaban hukumar Ilimi bai daya ta jihar Kano Malam Yusif Kabir, godewa Gwamnan yayi tare da yiwa daliban makarantun Firamare albishir na kawo karshen zaman su a kasa.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin kaddamar da raba kujerun zaman daliban nan bada jimawa ba dan fara cingajiyar su tare da bukatar kulawa da su yadda ya kamata dan a dade ana amfani da su.