Ana zargin Jami’an tsaro da harbe mutane huɗu tare da jikkata wasu 16, yayin atisayen rushe gine-gine da gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta gudanar a garin Rimin Zakara, dake kusa da Jami’ar Bayero ta Kano a ƙaramar hukumar Ungogo a jihar.
Aikin na rusau ɗin ya shafi gine-gine kimanin 18.
Al’amarin ya faru ne adaren lahadi, lamarin da ya haifar da turjiya daga mazauna yankin, inda suka ce ba a basu isasshiyar sanarwa ba kafin rushewar.
Malam Sunusi Dan-Baba, ganau ne ya shaida cewa tawagar rusau ta iso da daddare, inda suka fara ruguza gidaje da shaguna.
Ya ƙara da cewa ana takaddama kan mallakar filin unguwar tsakanin jami’ar Bayero ta Kano da mazauna yankin sama da shekaru 20 da suka gabata.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar tsaro da kare kadarorin gwamnati (NSCDC) reshen Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tura jami’an tsaro ne domin kare kadarorin gwamnati, sai mazauna yankin suka kai musu farmaki, inda suka raunata jami’i ɗaya, tare da lalata motocin su.
A bangaren ma’aikatar filaye da tsare-tsare ta jihar Kano, ta tabbatar da cewa filin na Jami’ar Bayero ne, kuma an bi duk hanyoyin doka kafin rusau din.
Daraktan yada labarai na ma’aikatar, Umar Abdu Kurmawa, ya ce an bayar da sanarwa tun kafin aiwatar da rusau din, har ma an biya diyya ga wadanda abin ya shafa sama da shekaru 20 da suka wuce.
Duk kokarin jin ta bakin Daraktan Hulda da Jama’a na Jami’ar Bayero, Malam Lamara Garba, bai yi nasara ba, domin wayarsaa a kashe take.