Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Gwamnatin Nijeriya ta janye dokar hana haƙar ma’adinai a Zamfara bayan shekaru biyar da kafawa
Afrika

Gwamnatin Nijeriya ta janye dokar hana haƙar ma’adinai a Zamfara bayan shekaru biyar da kafawa

December 23, 2024
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Gwamnatin Nijeriya ta janye dokar hana haƙar ma’adinai da ta sanya a jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar bayan shekaru biyar da kafa dokar.

Ministan haɓaka harkokin ma’adinai, Dele Alake, shi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai tare kuma da shafinsa na X ranar Lahadi.

Alake ya ce Nijeriya “za ta ci riba mai yawa idan aka ƙara farfaɗo da harkokin tattalin arziƙi a jiha mai ma’adinai da yawa kamar Zamfara wadda take da zinari da lithium da tagulla da yawa.”

“Gwamnatin Tarayya ta ɗage dokar da ta hana haƙar ma’adinai a jihar Zamfara saboda ƙarin sauƙi da aka samu kan lamarin tsaro a faɗin jihar,” in ji sanarwar da ministan ya fitar.

Ministan ya bayyana cewa dokar hana haƙar ma’adinai da aka yi, wadda take da niyya mai kyau, ta bar wani giɓi wanda masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’i’da ba suke amfani da shi wajen satar ma’adinan ƙasa.

Ya jaddada cewa jihar tana da yiwuwar samar wa da Nijeriya kuɗin shiga mai tarin yawa.

“Barazana ga rayuka da ta sa aka hana haƙar a shekarar 2019 ta ragu. Manyan nasarorin da jami’an tsaro suka samu sun samar da gagarumar raguwa ga rashin tsaro, kuma yanzu da aka ɗage dokar hana haƙar ma’aidinai, sannu a hankali fannin haƙar ma’adinai na Zamfara zai fara ba da nasa gudunmawar ga kuɗin shigar ƙasa,” a cewar Alake.

“Tun daga farkon gwamnatin Tinubu dai ayyukan jami’a tsaro wadda suke yi bisa bayanan sirri sun yi sanadin kashe manyan ɓarayin daji lamarin da ya rage matsalar tsaro,” in ji ministan.

Acewarsa dage wannan doka zai ba da damar tattara bayanan sirri domin daƙile haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba tare da tabbatar da cewa ƙasar ta amfana da arziƙin ma’adinan jihar.

Alake ya jaddada cewa yarjejeniyar da Nijeriya ta shiga da Faransa da ya janyo ce-ce-ku-ce kwanakin baya ba ya nufin ƙasar za ta sallamar da ma’adananta ko kuma ƙulla alaƙar soji da Faransa.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026

Maki shida ne ya rage tsakanin Arsenal da Man City

April 13, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.