Author: Wafsym

Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya ce ya yi atukar farin ciki da kamen da hukumomin Finland suka yi wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware ta IPOB ta Najeriya, Simon Ekpa. “Nayi farin ciki kwarai da gaske bisa kama wannan shugaban haramtacciyar yan aware da hukumomin tsaron finland sukayi, maisuna Simon Ekpa, wannan abun farin ciki ne so sai” Cikin wani saƙo da kakakin ma’aikata tsaron ƙasar, Manjo Janar Tukur Gusau ya aikowa DNN Hausa ya ce babban hafsan tsaron ƙasar ya ce yana fatan kamen ya zama wani mataki na tisa ƙeyar Mista Ekpa zuwa…

Read More

Kwamitin Musamman na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce hanyoyin yakin da Isra’ila ke bi a Gaza daidai suke da kisan kare dangi, ciki har da kisan fararen hula da ake yi da kuma wahalar da Falasdinawa. Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya afka wa yankunan kudancin babban birnin kasar Labanon bayan da Isra’ila ta gargadi mazauna yankin su fice daga wani bangare na sansanin Hezbollah, kamar yadda hotunan AFP suka nuna. Wani hayaki mai launin toka ya turnuƙe yankin bayan harin na baya-bayan nan tun bayan da Isra’ila ta tsananta kai hare-haren bam a Lebanon a watan…

Read More

Shugaban Karamar hukumar Rimin Gado Hon. Muhammad Sani Salisu Jili ya ce karamar hukumar ta kuduri aniyar samarwa da matasa ayyukan yi musamman ta fannin bun kasa harkokokin noma ta yadda za su tsaya da kafafun su. Muhammad Sani Salisu Jili ya bayyana haka yayin zantawar sa da wakilin sashen Hausa na DNN. Ya kara da cewa za su mayar da hankali wurin kulawa da iyaye mata domin kula da kawunan su ta fannin samar mu su da sana’oin dogaro da kai. Acewarsa idan aka gina mace daya tamkar an gina al’umma ne, domin ta kar kashinta kadai za’a kara…

Read More

Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta kafa kwamitin ƙwararru da zai yi aikin yiwa baƙi ƴan ƙasashen waje mazauna birnin rijista, musamman waɗanda suke gudanar da kasuwanci. Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne domin samun alƙaluman mutanen da suka fito daga ƙasashen ƙetare kuma suke gudanar da harkokin kasuwanci a jihar ta yadda za’a haɓɓaka kudin shiga da kuma tsaro da samar da ayyukan yi. Kwamitin da ke ƙarƙashin ofishin sakataren gwamnatin Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi, zai tattara bayanan baƙin da ke aiki walau na kamfani ko a wata ma’aikata ko kuma kasuwanci. Shugaban kwamitin, Lawan Isa…

Read More

Babbar Kotun Tarayyar Najeriya da ke Abuja ta soke ƙarar da aka shigar gabanta kan zargin da ake yi wa wasu yara ‘yan da cin amanar ƙasar bayan sun gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa mai taken #EndBadGovernance a watan Agustan shekarar 2024. Alƙalin kotun, mai shari’a Obiora Egwuatu, a ranar Talata ya soke ƙarar bayan M. D Abubakar, lauyan Antoni Janar na Nijeriya ya shigar da buƙatar janye tuhumar baki daya. Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci kotu ta saki ƙananan yaran da aka gurfanar a gabanta, waɗanda suke cikin mutanen…

Read More

Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta yi watsi da rahotannin da ake yaɗawa cewa akwai rashin jituwa tsakanin Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf da kuma jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. A ranar Litinin ne jaridar Daily Nigerian ta fitar da wani labari wanda ke zargin cewa gwamnan Kano Abba Kabir ya daina ɗaukar kiran wayar uban gidansa Sanata Rabiu Kwankwaso, lamarin da hakan ya tayar da ƙura a kafofin sada zumunta. Sai dai a wata sanarwa da babban mai taimakawa gwamnan Kano kan kafofin sada zumunta Salisu Yahaya Hotoro ya fitar, ya ce babu wata rashin jituwa tsakanin…

Read More

Jamal Musiala ya dawo kuma zai bi tawagar Bayern zuwa Spain a wasan da zasu fafata da Barcelona ranar Laraba. Jaridar AS ta rawaito Joan Laporta bai manta da dokewar da Bayern ta yi musu da ci (8-2) ba, lokacin da Flick yake horas da ƙungiyar ta Germany kuma Laporte ya nemi da ya rama hakan a wasa na gaba. Flick ya mayar masa da martanin cewa ko da basu rama 8 ba idan suka samu nasara ya wadatar. Yanzu haka Ƙungiyar Vincent Kompany ta buga wasanni 10, inda ta zura ƙwallaye 37 ya yin da aka zura mata ƙwallaye…

Read More

Real Madrid na kara kaimi wajen zawarcin Alexander-Arnold amma Liverpool na fatan za ta shawo kan dan wasan mai shekaru 26 ya ci gaba da zama. Dan wasan bayan na Liverpool Arnold, mai shekara 26, zai iya barin Anfield don komawa Real Madrid a kyauta, yayin da amininsa Jude Bellingham ke ta kokarin gamsar da shi ya yi hakan. Jurgen Klopp ya zama sabon shugaban ƙwallon ƙafa na dukkan ƙungiyoyin rukunin Red Bull da ke faɗin duniya. Jurgen Klopp zai fara aiki daga Janairun 2025 akan kujerar, wadda zata bashi damar bayar da shawarwari ga dukkan ƙungiyoyin Red Bull, kama…

Read More

Shugaban hukumar Alhazan Najeriya NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya bayyana cewa hukumar tana iya bakin ƙo ƙarinta domin tabbatar da kuɗin hajjin bana bai kai yadda ake hasashe ba, wanda ya ce abin da yake fata shi ne a samu sauƙi. Hukumar ta NAHCON ce ta sanar da cire tallafin da take bayarwa a kan kuɗin Hajjin ko wace shekara, wanda a sanadiyar hakan masana suka ce kuɗin kujerar Hajjin zai iya haura naira miliyan 10 duk mutum ɗaya. Abdullahi Pakistan, ya ce “ba ma fatan a samu ƙarin kuɗin kujerar Hajji kamar yadda ake hasashe, za mu…

Read More

Wata Dorinar ruwa ta hallaka mai gadin wani gidan gona da ake kira gidan gonar Orchard, mallakin Sarkin Yauri, Dr. Muhammad Zayyanu Abdullahi. Mai gadin maisuna Malam Usman Maigadi, ya rasa rashi ne lokacin da ya shiga kogin Yauri dake kauyen Tillo a jihar Kebbi yana kamun kifi. Rahotanni sunce dorinar ruwan ta farmaki mai gadin mai kimanin shekaru 60 a duniya lokacin da tayi zaton yaje ne zai ɗaukar mata ɗanta, saboda haka itama saita afka masa a wani salo na kare kai daga daukar mara da ko dauka. Shugaban karamar hukumar Yauri, Alhaji Abubakar Shu’aibu ya tabbatar da…

Read More