Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta kafa kwamitin ƙwararru da zai yi aikin yiwa baƙi ƴan ƙasashen waje mazauna birnin rijista, musamman waɗanda suke gudanar da kasuwanci.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne domin samun alƙaluman mutanen da suka fito daga ƙasashen ƙetare kuma suke gudanar da harkokin kasuwanci a jihar ta yadda za’a haɓɓaka kudin shiga da kuma tsaro da samar da ayyukan yi.
Kwamitin da ke ƙarƙashin ofishin sakataren gwamnatin Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi, zai tattara bayanan baƙin da ke aiki walau na kamfani ko a wata ma’aikata ko kuma kasuwanci.
Shugaban kwamitin, Lawan Isa Kibiya ya ce aikin da za su yi zai taimaka wajen tabbatar da ganin baƙin waɗanda mafi yawa ƴan kasuwa ne su na biyan haraji kamar yadda doka ta yi tanadi.
Ya ƙara da cewa hakan zai bai wa gwamnati ƙwarin gwiwar ‘‘ƙoƙarin ganin ta samar da yadda za ta ba su kariya ta fuskar tsaro’’
Kwamishinan ma’aikatar ciniki ta jihar Kano, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya wanda wakili ne a kwamtin ya ce ‘‘aikin bai taƙaita ga buƙatar tattara haraji kaɗai ba, duk duniya akwai ƙa’idoji da aka kafa a doka, waɗanda idan baƙo ya je zai yi kasuwanci ga ƙa’idojin da ya kamata ya bi, sannan su ma ƴan gari ga ƙa’idojin da ya kamata su bi.’’
Ya ƙara da cewa ‘‘idan ka shiga wannan manyan kasuwannin namu, musamman kantin kwari, za ka ga baƙin su ne mafi yawa ke ƙerawa, su yi packaging su kuma yi kasuwanci kai tsaye.’’
Adamu Kibiya, ya kara da cewa ire-iren waɗannan abubuwan gwamnati ta kalla shi yasa ake ƙoƙarin fito da tsarin da zai taimaki al’umma musamman wajen samar da ayyuka da kare martabar kasuwanci: ‘‘Idan muka zura ido mu ka yi gaba to zai zamo nan gaba mun koma maula, mutanen mu sun koma bara, don haka gwmanati ta duba, ta ga dole wadannan abubuwa an taka musu birki.’’
Ya ƙara da cewa tsarin zai tsaftace harkokin kasuwanci a jihar, musamman yadda aka saba samun masu yi wa ƴan kasuwa zambo domin kwashe musu kuɗi, kuma ana samun irin waɗannan bata gari masu aikatawa daga kowanne ɓangare.
Toh sai dai kwamitin ya tabbatar da cewa rijistar ba ta shafi ƴan wasu jihohin da suke zaune a jihar Kano ba, inda ake fatan nan da makonni biyar kwamitin zai mikawa gwamnati rahotansa.