Shugaban hukumar Alhazan Najeriya NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya bayyana cewa hukumar tana iya bakin ƙo ƙarinta domin tabbatar da kuɗin hajjin bana bai kai yadda ake hasashe ba, wanda ya ce abin da yake fata shi ne a samu sauƙi.
Hukumar ta NAHCON ce ta sanar da cire tallafin da take bayarwa a kan kuɗin Hajjin ko wace shekara, wanda a sanadiyar hakan masana suka ce kuɗin kujerar Hajjin zai iya haura naira miliyan 10 duk mutum ɗaya.
Abdullahi Pakistan, ya ce “ba ma fatan a samu ƙarin kuɗin kujerar Hajji kamar yadda ake hasashe, za mu yi duk mai yiwuwa wajen ganin hakan bata faru ba, haka kuma muna fatan insha Allahu ba zai kai haka ba.
“Abin da muke fata shi ne a samu ragowa daga farashin kuɗin kujerar da aka biya a bara, kuma muna fata da yardar Allah za mu samu nasara.”
Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan na wannan jawabin ne mako guda da shigarsa ofis domin fara aiki gadan-gadan.