Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya ce ya yi atukar farin ciki da kamen da hukumomin Finland suka yi wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware ta IPOB ta Najeriya, Simon Ekpa.
“Nayi farin ciki kwarai da gaske bisa kama wannan shugaban haramtacciyar yan aware da hukumomin tsaron finland sukayi, maisuna Simon Ekpa, wannan abun farin ciki ne so sai”
Cikin wani saƙo da kakakin ma’aikata tsaron ƙasar, Manjo Janar Tukur Gusau ya aikowa DNN Hausa ya ce babban hafsan tsaron ƙasar ya ce yana fatan kamen ya zama wani mataki na tisa ƙeyar Mista Ekpa zuwa Najeriya dominn ya fuskanci shari’a.
A ranar Alhamsi ne hukumomin Finland suka kama Simon Ekpa tare da aika shi gidan yarin ƙasar, byan gurfanar da shi a kotu, kan zargin tunzura mutane su aikata ayyukan ta’addanci.
Kotun ta ce ta samu Simon Ekpa ne da laifin yaɗa aƙidu na ƴan aware a kafar sada zumunta, a ranar 23 ga watan Agustan shekarar 2021 a birnin Lahti na ƙasar ta Finland.
Yan Najeriya da dama sunyi farin ciki da kama Ekpa, inda suke fatan shari’a zatayi aiki akanshi kuma kamen da akayi masa zai taimaka wajan karya kungiyar ta yan aware a Najeriya.