Babbar Kotun Tarayyar Najeriya da ke Abuja ta soke ƙarar da aka shigar gabanta kan zargin da ake yi wa wasu yara ‘yan da cin amanar ƙasar bayan sun gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa mai taken #EndBadGovernance a watan Agustan shekarar 2024.
Alƙalin kotun, mai shari’a Obiora Egwuatu, a ranar Talata ya soke ƙarar bayan M. D Abubakar, lauyan Antoni Janar na Nijeriya ya shigar da buƙatar janye tuhumar baki daya.
Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci kotu ta saki ƙananan yaran da aka gurfanar a gabanta, waɗanda suke cikin mutanen da gwamnatin ta zarga da cin amanar kasa – lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce da muhawara mai zafi a ƙasar.
Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa Antoni Janar na ƙasar, Lateef Fagbemi, damar janye ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar a gaban kotu ta hanyar karɓe lamarin daga hannun Babban Sufeton ‘Yan sandan kasar.
Daga nan ne Mai Shari’a Egwuatu ya soke ƙarar abin da ke nufin an wanke mutum 119 daga zargin da gwamnati ta yi musu na cin amanar ƙasa.
Ko da yake mutanen ba su bayyana yau a gaban kotun ba, inda alƙalin ya yi umarni a sake su daga gidan yarin da ake tsare dasu nan-take.