Shugaban Karamar hukumar Rimin Gado Hon. Muhammad Sani Salisu Jili ya ce karamar hukumar ta kuduri aniyar samarwa da matasa ayyukan yi musamman ta fannin bun kasa harkokokin noma ta yadda za su tsaya da kafafun su.
Muhammad Sani Salisu Jili ya bayyana haka yayin zantawar sa da wakilin sashen Hausa na DNN.
Ya kara da cewa za su mayar da hankali wurin kulawa da iyaye mata domin kula da kawunan su ta fannin samar mu su da sana’oin dogaro da kai.
Acewarsa idan aka gina mace daya tamkar an gina al’umma ne, domin ta kar kashinta kadai za’a kara haifar da dubban mata da maza da zasu taso da abunyi a hannu.
“A shirye wannan karamar hukuma take taga ta taimaki rayuwar mata duba da irin raunin da suke da shi a hannu guda kuma suna da matukar muhimmanci da gudunmawar bayarwa”.
A matsayina na matashi banida burin da ya wuce na taimaki rayuwar matasa kamar yadda jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taimaki rayuwata, Inji Jili.