Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Shugabannin Ecowas za su gana a Abuja
Afrika

Shugabannin Ecowas za su gana a Abuja

December 15, 2024
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
d43c9133 d6ee 4e49 8fca f7d6de68a224.jpg
d43c9133 d6ee 4e49 8fca f7d6de68a224.jpg

Shugabannin ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas za su gana yau Lahadi a Abuja, domin tattauna batutuwan da suka shafi haɗin kai da tsaro da kuma tattalin arzikin yankin.

Ana sa ran batun ficewar ƙasashen yankin Sahel daga ƙungiyar ne zai zama babban ajandar taron na yau.

Ƙa’idar da Ecowas ta gindaya ta sanarwar shekara guda kafin ficewar ƙasa daga ƙungiyar – wanda ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar suka yi – zai cika a watan Janairu mai zuwa.

A makon da ya gabata ne, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya shaida wa shugaban Jamus da ya ziyarci ƙasar, Frank-Walter Steinmeier, cewa muradun walwalar ‘yan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar ne babban abin da ke ran shugabannin Ecowas.

Inda ya alƙawarta yi amfani da diplomasiyya da hikima wajen maido da ƙasashen cikin ƙungiyar.

Shugaba Tinubu – wanda shi ne shugaban Ecowas – ya sha amfani da hanyoyin diflomasiyya don ganin ya janyo hankalin ƙasashen na yankin Sahel domin su koma cikin ƙungiyar.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026

NAPTIP Ta Ceto Mata Bakwai Ake Zargin Ana Shirin Safarar Su zuwa Ƙasar Iraki A Kano ‎

February 12, 2026

Tirela Ta Murkushe Mutum Biyu Har Lahira A kaduna  ‎

February 12, 2026

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf A Matsayin Shugaban NAHCON

February 11, 2026

Mata sun fi maza yin aikin baban-giwa a Najeriya

February 11, 2026

Dalilin Da Ya Sa Na Ajiye Shugabancin NAHCON – Abdullahi Saleh Pakistan

February 11, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

By WafsymFebruary 12, 2026

A daidai lokacin da ya rage ‘yan kwanaki kaɗan a shiga watan Ramadan mai alfarma,…

‎“Ya Kamata ‘Yan Jaridu Su Riƙa Nuna Tausayi, Hikima Da Mutunta Jinƙan Ɗan Adam wajen ɗauko labarai ‎ ‎ ‎—Comrade Abbas Ibrahim

January 21, 2026

‎Kisan Gilla: Shawarwari Ga Mata Masu Zaman Gida Don Kare Rayukansu

January 19, 2026

‎Sauyin Yanayi Na Canza Yanayin Sanyi A Arewacin Najeriya  ‎ ‎ ‎— Masana ‎

January 18, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.