Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi maraba da sulhun da aka yi tsakanin Kasashen Ethiopia da Somalia wanda Turkiyya ta jagoranta a birnin Ankara.
An gudanar da taron sulhun ne a ranar Laraba.
Turkiyya ta jagoranci sulhun ne tsakanin ƙasashen biyu da ke maƙwabtaka da juna bayan sun kwashe kusan shekara guda suna tayar da jijiyoyin wuya.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, wanda ya karɓi baƙuncin Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed da shugaban ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ranar Laraba, ya bayyana sulhun a matsayin wanda ke cike da “tarihi.”
A ranar Alhamis, Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat, ya bayyana sulhun a matsayin wani mataki “mai matuƙar muhimmanci da nuna dattako a tsakani.”