Shugaban majalisar wakilan Najeriya Tajuddeen Abbas, ya ce matakan da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu yake ɗauka wajen inganta tattalin arzikin Najeriya na nuna yadda shugaban ya damu da damuwar al’ummar ƙasar.
Abbas ya bayyana hakan ne a jawabinsa a lokacin da shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024 a gabatan majalisar dokokin ƙasar a ranar Laraba.
“Majalisar dokoki za ta ci gaba da goyon bayan matakan gyare-gyaren da kake ɗauka ta hanyar yin dokoki da kuma tattaunawa tare da wayar da kan mutane domin ƙara fahimta da amincewa” Inji Abbas
Ya ƙara da cewa tafiye-tafiyen da shugaban yake yi sun ƙara ɗaga darajar ƙasar a idon Duniya.
“Sai dai ana buƙatar irin wannan sadaukarwar domin ƙasa ta ci gaba.”
Sai dai ya ce akwai buƙatar a yaba da sadaukarwa da ƴan Najeriya suka nuna, inda ya ce cire tallafin man fetur da hauhawar farashin kayayyaki da wasu matakan inganta tattalin arziki sun haifar da ƙalubale sosai.