Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Aikin Hajjin 2025 Zai Gudana Cikin Tsari Da Nasara – NAHCOON
Arab

Aikin Hajjin 2025 Zai Gudana Cikin Tsari Da Nasara – NAHCOON

December 12, 2024
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
WhatsApp Image 2024 12 12 at 14.31.57
WhatsApp Image 2024 12 12 at 14.31.57

A wata ganawa da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya jaddada aniyarsa na gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025 cikin tsari da nasara.

Ahugaban ya bayar da tabbacin ne a jawabinsa yayin wani taro da aka gudanar a hedikwatar hukumar NAHCON da ke Abuja.

Farfesa Pakistan ya nuna godiya ga Allah da ya ba da damar gudanar da taron tare da jaddada sadaukarwar hukumar wajan shawo kan kalubale da kuma sake mayar da hankali domin samun damar inganta aikin hukumar.

A cikin jawabinsa, shugaban ya bayyana kalubale da dama da ya tarar lokacin da aka naɗa shi mukamin da suka haɗa da iƙrarin da ba a warware ba da kuma cikas wajen gudanar da ayyukan da suka kawo tasgaro ga ci gaban wasu muhimman ayyuka.

Ya kuma baiwa masu ruwa da tsaki tabbacin ci gaba da kokarin shawo kan matsalolin.

“Alhamdulillah, a yau dukkanmu muna nan a matsayin abokan aiki, muna haɗa kawunanmu wuri guda domin magance ƙalubalen da ke gabanmu da kuma yin aiki a matsayin wata babbar ƙungiya domin tallafawa ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci,” inji Farfesa Pakistan.

Har ilayau ya bayyana wasu daga cikin batutuwan da ake ta cece-kuce da su kawo yanzu, wanda suka haɗa da mayar da Riyal 150 na Saudiyya da rashin da wutar lantarki ingantacciya a lokacin aikin Hajjin 2023.

Farfesa Abdullahi Pakistan ya tabbatar da cewa shugabancinsa na aiki tuƙuru domin ganin an daidaita kuɗaɗen hidimar kashi 2% da aka warewa hukumar alhazai ta jiha dangane da aikin Hajjin 2024.

Shugaban ya kuma yi alƙawarin biyan duk kanin wasu haƙƙoƙi da aka nema waɗanda suka yi daidai da doka, tare da aza harsashin wani sabon babi na ayyukan NAHCON.

Farfesa Saleh ya yi kira ga shugabannnin hukumomin alhazai na jahohi dasu gaggauta sanya kuɗaɗe ga hukumar domin samun damar yin shiri da wuri da suka haɗa da samar da gidaje masu arha da dacewa a Madina, Makkah, Mina da Mashaer.

Ya kuma sanarwa da taron cewa zai fara ziyarce-ziyarce a shiyyoyin kasar nan guda shida domin tattaunawa da malaman addini da sarakunan gargajiya domin samun goyon baya da albarkar aikin Hajjin 2025 da kuma ziyarar farko kafin aikin Hajji a kasar Saudiyya wanda zai gudana a watan Janairun 2025 wanda ya ƙunshi wakilai daga NAHCON da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi wadanda za su halarci tarukan shirye-shiryen aikin Hajji, tare da kammala yarjejeniya da hidimar alhazai, da kuma duba shirye-shirye a Jeddah.

Shugaban hukumar ta NAHCON ya kuma jaddada muhimmancin haɗa kai, inda ya bayyana ma’aikatan NAHCON da shuwagabannin masu ruwa da tsaki na jahohi a matsayin manyan ginshiƙan hukumar.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su hada kai a matsayin abokan aiki domin cimma manufa ɗaya ta samar da aikin Hajji mai cike da inganci ga alhazan Najeriya.

A cikin kalamansa, “Na zo nan ne da kyakkyawar niyya da kuma tsare-tsare masu yawa na kawo sauyi a fasalin Hukumar.

A jawabin Kwamishinan aiyuka na hukumar, Prince Anofi Olarewaju Elegushi ya bayar da bayanai kan kalandar Hajji ta 2025, inda ya bayyana cewa an raba takardar jagora mai shafuka 51 daga ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya don daidaita ayyukan.

Taron ya kuma tabo batutuwan da ba a warware su ba daga aikin Hajjin 2024 inda Kwamishinan hukumar mai Kula da Ma’aikata da Kudi (PPMF), Aliu Abdulrazak ya bayyana cewa Shugaban hukumar NAHCON ya ba da izinin fara biyan kuɗaɗen da Jihohi ke biya bayan an kammala sulhu da su da sashen kuɗi da Asusu.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026

Maki shida ne ya rage tsakanin Arsenal da Man City

April 13, 2026

Mutane sama da 50 sun rasu a kuskuren harin sojin sama a kasuwa

April 13, 2026

INEC ta ɗage aikin sabunta bayanan rajistar masu zaɓe a fadin ƙasa

April 11, 2026

Gwamnan Kano ya naɗa Bilkisu Maimota a matsayin shugabar ma’aikata ta jiha

April 11, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.