Kamfanin mai na Dangote dake Najeriya ya sanar da cewa a karon farko ya fitar da man fetur zuwa kasar Kamaru, wanda ake sa ran hakan zai buɗe wata hanya da za ta taimaka wurin samun wadataccen man fetur da kuma daidaita farashi a yankin.
Sai dai kamfanin na Dangote bai bayar da cikakken bayani kan ganga nawa ya fara fitarwa zuwa kasar ba.
Kamfanin samar da makamashi na kasar Kamaru Neptune Oil a cikin wata sanarwar da ya fitar ya bayyana cewa, duk kanin kamfanonin biyu suna nazari domin samar da tsare-tsare waɗanda za su taimaka wajen daidaita farashin man fetur da samar da damammaki a yankin.
Neptune Oil ya ce an aiwatar da cinikin samar da man ba tare da masu shiga tsakani ba.
Matatar man Dangote mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kullum na da burin yin gogayya da matatun mai na Turai idan ta soma aiki gadan-gadan.