Sabon shugaban hukumar Alhazan Nigeria NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya ci alwashin yin aiki tukuru domin tabbatar da gudanar da aiki mai tsafta tare da kawo cigaba a hukumar.
‘’Tafiyar da hukumar alhazan Najeriya NAHCON aiki ne mai girman gaske dake bukatar tayani da addu’a domin na samu karfin gwiwar tafiyar da aikin cikin gaskiya da amana” inji Farfesa Pakistan.
Shugaban hukumar ta NAHCON na wannan jawabin ne lokacin da gidauniyar cigaban Tudun Murtala dake jihar Kano a arewacin kasar ta kai masa ziyarar taya murna gidansa, bisa mukamin da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya bashi na suhagabantar hukumar alhazan NAHCON.
Yayin ziyayar, Farfesa Muhammad Binyamin Ado da Dagacin Dakata Alhaji Salisu Ibrahim sun bayyana cewa kujerar shugabancin NAHCON bata taba zuwa jihar Kano ba, saboda haka akwai bukatar taya Farfesa Pakistan murana da addu’ar samun ikon sauke nauyin al’ummar Najeriya.
“A matsayinka na dan Tudun Murtala kuma Allah ya baka wannan mukami, ya zama wajibi muzo a kungiyance mutayaka murna muyi maka fatan alkhairi” Injin Farfesa Muhammd Binyamin.
Lokacin da shugaban gidauniyar cigaban al’ummar Tudun Murtala Alhaji Yahya Umar Bagobiri ke nasa jawabin, godewa shugaban Nigeria Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shatima yayi bisa dora kwarya a gurbinta.
‘’Dole na godewa shugaban Nigeria Bola Tinubu da mataimakin Kashim Shattima bisa wannan babbar kujera daka bawa dan Tudun Murtala, kujerar da bata taba zuwa jihar Kano balle kuma wannan gari namu ba. Inji Yahaya Bagobiri
Shugaban hukumar ta NAHCOON Farfesa Abdullah Saleh Pakistan yayi alkawarin cewa ba zai bawa malamai da sauran al’umma kunya ba, bisa wannan nauyi da shugaban kasa ya dora masa.
‘’Tunda kuna ce min malam, ina mai tabbatar muku cewa da Sanina ko dagangan, bazan zubar da mutuncina ba kuma bazan taba baku kunya ba, domin duk abinda nayi mara kyau sai ya shafi wannan unguwa ta Tudun Murtala, domin babu abinda wannan gari na karramawa wanda baiyimin ba”Inji Shugaban na NAHCON.
Manyan mutane daga unguwar ciki hadda Farfesa Atiku da masu unguwanni, limamai da sauran al’ummar garin ne suka halarci ziyarar taya sabon shugaban hukumar ta NAHCOON Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan Murna.