Gwamnan Jihar Kano dake arewacin Najeriya, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da katafariyar kasuwar shanu a karamar hukumar Dambatta domin bunkasa harkokin kasuwanci a jihar Kano.
Gwamnan ya ce aikin kasuwar hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Kano da bankin raya Musulunci na Duniya.
Har ilayau ya ce an samar da irin wadannan kasuwannin guda biyar awasu daga cikin Kananan hukumomin Kano duk da tallafin Bankin raya Musulunci.
Haka zalika gwamnan ya kaddamar da hanya da ta tashi daga garin Dambatta zuwa garin Diggol, a wane mataki na yunkurin gwamnati na rage alummar yankin wahalhalun d ahanyar ka iya jawowa.
A wani Labarin kuma Gwamnan na Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake kaddamar da hanyar da ta tashi daga garin Minjibir zuwa Wasai zuwa Baita.
Yan kwangilar hanyar sun tabbar da zasu kammala aikin nan da watanni shida masu zuwa.