Gwamnan Jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum ya bayyana alakar dake tsakanin Jihar Kano da Maiduguri da cewa tsohuwar alaka ce Mai tsohon tarihi.
Gwamnan Babagana Zulum ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan Gwamnati bisa rakiyar Shehun Borno Alhaji Abubakar ibn Umar Garbai El Kanemi a ziyar jajantawa da Sarkin Kanon ya Kai Jihar Borno.
Gwamna Zulum ya godewa mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero bisa wannan ziyara da ya Kai musu inda yace bazasu taba mantawa da wannan ziyara ba kuma zata Kara karfafa zumuncin dake tsakanin jihohin guda biyu.
Ya bayyana irin asarar rayuka da dukiyoyin da al’umar jihar Borno sukayi da cewa wata babbar asara ce da bazasu iya misalta ta ba Amma yace wata jarrawace daga Allah Yana Mai Kara godiya ga Allah da Gwamnatin Tarayya da al’umar Najeriya bisa tallafi da addu’oin da akayi musu.
A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace yace ya ziyarci garin Maiduguri ne domin jajantawa al’umar jihar Borno da Gwamnatin jihar da kuma Shehun Borno bisa wannan ibtila’i na ambaliyar ruwa data afku.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace a madadin al’umar jihar Kano dashi kansa suna Kara jajantawa wadanda suka gamu da wannan ibtila’i inda yayi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.
Mai Martaba Sarkin ya godewa al’umar jihar Borno bisa yadda suka karbeshi, inda yace wannan ba wani abun mamaki bane sakamakon yadda alakar zumunci take a tsakanin al’umar jihar Kano da kuma ta Maidugurin.
Tunda farko da yake jawabinsa lokacin daya karbi bakuncin Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa, Shehun Borno Alhaji Abubakar ibn Umar Garbai El Kanemi ya godewa Alhaji Aminu Ado Bayero bisa wannan ziyara daya kawo kafa da kafa garin na Maiduguri domin jajanta musu bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da suka samu.
Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai El Kanemi yayi addu’a da fatan cigaban zumuncinsu da dorewar zaman lafiya da karuwar arziki a jihohin nasu da Kasa baki daya