Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayana Dalilan yin Gwanjon motocin ta na aiki da suka tsufa.
Mai magana da yawun hukumar a nan Kano Sadiq Muhammad Maigatari,ne ya bayana hakan a zantawarsa da manema labarai.
Muhammad Maigatari, ya Kara da cewa, “mafi yawacin motocin da hukumar ke aiki da su dama Wanda suke tsaye a ofisoshin hukumar sun tsufa tare da wuce shekarun da ya kamata a ce suna aiki da su bisa doka”
Mai magana da yawun hukumar NDLEA a nan Kano Sadiq Muhammad Maigatari, ya kuma ce,”cigaba da aiki da tsafin motocin da suka wuce shekara takwas barazana ne ga aikinsu da rayuwar ma’aikatansu musamma lokacin da sukaje aikin kamo masu sha, dillaci ko safarar miyagun kwayoyin sakamakon lalacewa da motocin ke yi a wasu lokutan kan hanyar kai wanda ake zargi kotu ko dawowa ofishin su bayan sun gama kai sumame guraren da ake ta’ammali da miyagun kwayoyin”
Sadik ya kuma musanta zargin da wasu keyi cewa a jihar Kano ne kawai akayi gwanjon motocin yana mai cewa “Anyi gwanjon duk motocin da suka haura shekaru takwas ana aiki da su a ofisoshin hukumar ta NDLEA dake fadin kasar nan.