Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Gwamnatin Kano ta bada umarnin binciko dalilin yankewa ma’aikatan jihar kudadensu na albashi
Afrika

Gwamnatin Kano ta bada umarnin binciko dalilin yankewa ma’aikatan jihar kudadensu na albashi

February 27, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana takaicinsa kan rahotannin da suka nuna ana rage albashin wasu ma’aikatan gwamnati ko kuma hana su albashinsu gaba ɗaya, yana mai cewa hakan babban cin zarafi ne ga haƙƙin ma’aikata kuma cin amanar jama’a.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.

Gwamna Yusuf, wanda ya nuna matuƙar ɓacin ransa kan labarin cewa wasu ma’aikata sun kwashe watanni ba tare da an biya su haƙƙinsu ba, ya yi alkawarin binciko masu hannu a wannan aika-aika tare da ɗaukar matakin da ya dace a kansu.

“Wannan gwamnati ba za ta lamunci zalunci ga ma’aikata ba. Duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika, doka za ta yi aiki a kansa ba tare da rangwame ba,” in ji gwamnan.

A wani mataki na kawo ƙarshen wannan matsala, gwamnan ya kaddamar da wani kwamitin bincike mai ƙarfi don gano musabbabin matsalar, ko dai matsalar fasaha ce ko kuma ganganci da gangan da wasu suka aikata.

Kwamitin zai gudanar da bincike na musamman kan albashin ma’aikatan gwamnati daga Oktoba 2024 zuwa Fabrairu 2025, domin gano waɗanda abin ya shafa, tantance irin asarar da aka yi, tare da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar da kuma hukunta masu hannu a ciki.

Kwamitin mai mambobi bakwai, wanda Hon. Abdulkadir Abdussalam, Kwamishinan Harkokin Karkara da Ci gaban Al’umma, kuma tsohon Akanta-Janar na Jihar Kano ke jagoranta, ya ƙunshi ƙwararru a fannin kuɗi da tsarin biyan albashi.

Ga cikakken jerin mambobin kwamitin:l

1. Hon. Abdulkadir Abdussalam – Shugaban Kwamitin
Kwamishinan Harkokin Karkara da Ci gaban Al’umma

2. Dr. Bashir Abdu Muzakkari – Memba
Mai Bai wa Gwamna Shawara Kan Tattalin Arzikin Zamani (Digital Economy)

3. Dr. Aliyu Isa Aliyu – Memba
Daraktan Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano

4. Dr. Hamisu Sadi Ali – Memba
Daraktan Hukumar Sarrafa Basussuka ta Jihar Kano

5. Hajiya Zainab Abdulkadir – Memba
Daraktar Cibiyar Kwamfuta ta Jihar Kano

6. Aliyu Muhammad Sani – Sakataren Kwamitin
Daraktan Bincike da Tantancewa, Ofishin Sakataren Gwamnati

7. Ummulkulthum Ladan Kailani – Mataimakiyar Sakataren Kwamitin
Babbar Mataimakiyar Sakataren Gudanarwa, Ofishin Sakataren Gwamnati

An ba wa kwamitin wa’adin kwana bakwai kacal domin ya kammala bincikensa tare da gabatar da cikakken rahoto kan masu hannu a lamarin, girman barnar da aka yi, da kuma hanyoyin magance matsalar gaba ɗaya.

Gwamna Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki don tabbatar da Adalci, gaskiya, da biyan albashi cikin lokaci, yana mai cewa duk wanda aka samu da laifi ba zai tsira ba.

“Zamanin cin zarafin ma’aikata ya ƙare. Wannan gwamnati ce ta gaskiya da riƙon amana, kuma duk wani da aka samu da hannu a wannan aika-aika ba zai tsira ba,” in ji gwamnan.

Kwamitin binciken na fatan gano duk wata badakala da aka tafka a tsarin biyan albashi, tare da dawo da martabar tsarin albashi a Kano domin kare haƙƙin ma’aikata.

Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ne ya kaddamar da kwamitin a madadin mai girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita dake Karamar Hukumar Dutsenma a Jihar Katsina ta tuna da Marigayi Isa Kaita

July 2, 2025

Gwamnatin jihar Kano ta umarci masu gudanar da sana’ar gwangwan da su dakatar da sayo kayayyakin daga yankin Arewa maso Gabas

July 2, 2025

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban Najeriya – Barau I Jibrin

June 26, 2025

Karya dokar Tuki ke Jawo Asarar Dukiya da Rayuka Sakamakon Haifar da Hatsari

June 18, 2025

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya dawo gida Najeriya Bayan gudanar da Ibadar aikin Hajji 2025.

June 18, 2025

Gwamnatin jihar kano tayi kira ga iyaye da su dinga sanya idanu akan ƴaƴan su mata wajen sauke duk wani nauyi da yake kan su

May 28, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Kano

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

By WafsymApril 13, 2025

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayana Dalilan yin Gwanjon…

Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin Film ko waka a Kano

January 20, 2025

Madrid ko Barca: Wa zai lashe Spanish Super Cup?

January 12, 2025

Barca ta kara rashin nasarar ɗaukaka kara kan yi wa Olmo rijista

December 31, 2024
© 2025 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.