Gwamnatin jihar Kano ta ce zata gudanar da bincike bayan gano wani guri da take zargin ana yin aikin tashar saukar jirgin sama ba bisa kaida ba tare da rufe hanyar da manoma ke zuwa gonakinsu a garin Tiga dake karamar hukumar Bebeji.
Sakataren kwamitin gwamnatin Kano dake yaki da gine-gine ba bisa kaida ba Hamid Sidi Ali, shi ne ya bayana hakan ga manema labarai lokacin da kwamitin ya ziyarci gurin da ake aikin da safiyar ranar Jumma’a.
Wasu cikin masu gonaki a yankin sun bayana cewa tun lokacin da aka fara aikin da suke zaton tashar jirgin sama ce aka toshe hanyoyin da zata sadasu da gonakinsu cikin sauki.
Yanzu haka dai kwamitin na kartakwana dake yaki da gine-gine ba bisa kaida ba ya sanya alamomin gargadi da nufin dakatar da aikin tare da bude hanyar da manoma ayankin zasu cigaba da bi zuwa gonakinsu har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan lamarin.