El Rufai ya ce kamawa da tsarewa harma da kuma azabtar da abokan adawar siyasa ba wani sabon abu ba ne a rayuwa, saboda an taɓa tsare shi har sau 3 a baya sakamakon bayyana ra’ayoyinsa akan gwamnatocin da suka gabata.
Saboda haka, tsohon gwamnan ya ce kame da azabtarwar ba wani sabon abu bane, kuma Allah kadai ke sanyawa Bil Adama lokacin barin duniya.
El Rufai ya shaidawa mutanen da ya ce basa bacci duk lokacin da yake Nijeriya da su ƙwan da sanin cewar yana kan hanyar komawa kasar domin halartar bikin ƙaddamar da littafin tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Babangida da za’ayi a ranar 20 ga watan nan.
Tsohon gwamnan ya ƙarƙare da cewar su ga Allah kadai suka dogara, kuma basa tsoron wani mahaluki wanda ba Allah bane, yayin da ya ce fatar su ita ce samun makoma ta gari, amma kuma su kan shiryawa fuskantar akasin haka.
Ya ce kafin ranar 20 ga watan Fabrairu zai dawo Najeriya, ya kuma ce ya dakatar da karatun da yake yi da kuma shirin koyon wasu harsuna zai dawo gida Najeriya, domin a cewarsa ba zai ci gaba da yin shiru ba.
El Rufai ya kuma ce kamawa da tsarewa da kuma azabtar da abokan hamayya a siyasa ba sabon abu ba ne, ”ni kaina an kama ni kuma an kulle ne sau uku a baya saboda bayyana ra’ayi na kan gwamnatocin baya.” a cewarsa.
”Na daɗe ina jin waɗannan raɗe-raɗin kan kama ni da tsare ni da kuma azabtar da ni a wani ɗakin azabtarwa da ke ofisihin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ( wurin da ake zargin an azabtar ta Emefiele domin ya bar aiki a matsayin gwamnan CBN), tun watan Yulin 2024 lokacin da aka fara yaɗa rahoton majalisar dokokin jihar Kaduna” in ji shi.