Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da kashe sojojinta goma a iyakarta da Burkina Faso
Afrika

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da kashe sojojinta goma a iyakarta da Burkina Faso

February 6, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Gwamnatin sojin ƙasar Niger ta tabbatar da cewa wani harin kwantar ɓauna da ‘yan ta’adda suka kai ya yi sanadin mutuwar sojojinta guda goma a kusa da iyakar ƙasar da Burkina Faso.

A wata sanarwa da gwamnatin sojin ƙasar ta karanto a ranar Laraba da dare, ta bayyana cewa an tura jami’ai zuwa yammacin ƙasar a ranar Litinin domin kama ɓarayin shanu a ƙauyen Takzat.

“A lokacin wannan aikin ne wani gungun masu laifi ya yi wa jami’an tsaron kwanton-ɓauna wanda hakan ya kai ga rasa sojojinmu goma,” in ji sanarwar.

Duk da cewa maharan sun yi ƙoƙarin guduwa amma sojojin sun kama tare da kashe 15 daga cikinsu.

Jamhuriyar Nijar tare da makwabtanta Burkina Faso da Mali sun kwashe fiye da shekaru 10 suna gwabza fada da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka hada da wasu masu alaka da al-Qa’eda da kuma kungiyar Daesh.

Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a dukkanin kasashen uku a shekarun baya-bayan nan, mahukuntan kasar sun kori sojojin Faransa tare da karkata zuwa ga rundunonin sojojin haya na kasar Rasha domin neman taimakon tsaro.

Kasashen uku sun sha alwashin karfafa hadin gwiwarsu ta hanyar kafa sabuwar kawancen tsaro, wato kawancen kasashen Sahel ta AES.

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Za mu mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin ruwanmu – Koriya ta Kudu

May 11, 2026

Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja – Pantami

May 11, 2026

Dangote na shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya

May 11, 2026

Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano

May 5, 2026

Pantami ya yi watsi da tsarin maslaha bayan kin daukar shi a matsayin dan takarar gwamnan Gombe

May 3, 2026

Kwankwaso da Obi sun koma jam’iyyar NDC

May 3, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.