Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) reshen Kano ta aike da jami’ai 1,889 domin gudanar da aiki na musamman a lokacin bukukuwan karamar sallah da nufin tabbatar da ingantacciyar zirga-zirga da kare lafiyar matafiya a manyan hanyoyi.
Kwamandan hukumar a Kano, Ibrahim Abdullahi Matazu, ya bayyana cewa wannan shiri zai gudana daga ranar 27 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, tare da hadin gwiwar jami’ai 1,348 na dindindin da 541 na musamman.
Jami’an za su kula da zirga-zirga, aiwatar da dokokin hanya, da kuma bayar da agajin gaggawa ga wadanda suka tsinci kansu a hatsari.
Matazu ya bukaci direbobi su kiyaye dokokin hanya, yana gargadin su da guje wa tukin ganganci, tukin yara ƙanana, da tseren mota a lokacin bukukuwan.
“Hukumar FRSC reshen Kano na yi wa al’ummar jihar fatan yin bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali da aminci,” in ji shi.