An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana.
Mai Alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad III, ne ya bayyana haka a yau Asabar a Sakkwato.
Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadan nan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.
Muna yiwa dimbin musulmin duniya barka da sallah.