Kwamitin Aikin Hajji da Shugaban Ghana John Dramni Mahama ya kafa domin sake nazari kan kuɗin Aikin Hajjin bana ya sanar da rage kuɗin Aikin Hajjin daga GH¢75,000 zuwa GH¢62,000.
Kwamitin ya bayyana cewa an rage kuɗin Aikin Hajjin ne domin cika alƙawarin da Shugaba John Dramani Mahama ya ɗauka domin sauƙaƙa wa musalman kasar.
Haka kuma kwamitin ya bayyana cewa an samu nasarar wannan rangwamen ne bayan da shugaban ƙasar ya aika wata tawaga zuwa ƙasar Saudiyya, domin sabunta tattaunawa da mahukuntan ƙasar kan tsare-tsaren aikin hajjin bana ciki har da batun kuɗaɗe.
A yayin da yake magana kan wannan batu, shugaban kwamitin da sake nazari kan kuɗin Aikin Hajjin Alhaji Collins Dauda wanda shi ne ɗan majalisa da ke wakiltar Asutifi South a yankin Ahafo ya jaddada irin kyakkyawan kudiri da shugaban Ghana ke da shi kan sauƙaƙa wa maniyyata ta ɓangaren kashe kuɗi.
Dama tun a lokacin yaƙin neman zaɓe shugaban na Ghana ya yi alƙawarin sauƙaƙa wa maniyyata.