Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎
Babban Labari

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260629 WA0009

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta ƙara bai wa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) tallafi, ciki har da samar da ƙarin motocin aiki, domin ƙarfafa yaƙi da safara da kuma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.

‎Wannan na ƙunshe ne a saƙon Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Faruq Ibrahim, ya gabatar yayin bikin ƙona fiye da tan 12 na miyagun ƙwayoyin da aka ƙwace bayan kotu ta ba da umarnin lalata su.

‎An gudanar da bikin ne a yankin Kalebawa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano.

‎Gwamnan ya ce yaƙi da miyagun ƙwayoyi ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, yana buƙatar haɗin kan al’umma domin dakile matsalar da ke barazana ga rayuwar matasa da zaman lafiyar jama’a.

‎Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da fito da sabbin tsare-tsare da shirye-shirye da za su taimaka wajen rage yawaitar safara da amfani da miyagun ƙwayoyi.

‎A nasa jawabin, Shugaban Hukumar NDLEA na Ƙasa, Janar Muhammad Buba Marwa (mai ritaya), wanda Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar (DCG) Ahmad Sulaiman Ningi ya wakilta, ya yi kira ga gwamnatin jiha, ƙananan hukumomi, hukumomin tsaro da ƙungiyoyi masu zaman kansu su ci gaba da haɗa kai da NDLEA wajen yaƙi da matsalar miyagun ƙwayoyi.

‎Shi ma Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Dahiru Lawan Yahaya, ya bayyana cewa tabar wiwi ce ta fi rinjaye a cikin miyagun ƙwayoyin da aka lalata, tare da wasu nau’ikan ƙwayoyi da aka ƙwace daga hannun masu laifi.

‎Ya ƙara da cewa ana gudanar da lalata miyagun ƙwayoyin ne a bainar jama’a ne kawai bayan samun sahalewar kotu, domin tabbatar da gaskiya da bin doka.

‎Bikin ƙona miyagun ƙwayoyin ya samu halartar kwamandojin NDLEA daga jihohin maƙwabta, shugabannin hukumomin tsaro, ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki masu goyon bayan yaƙi da safara da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

“Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

July 11, 2026

Sarkin Gaya: Mallakar Katin Zaɓe Shi Ne Ginshiƙin Zaɓen Shugabanni Nagari

July 3, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rushe Tsarin Karatu Mai Dauke Da JSS Da SS A Makarantun Sikandire A Najeriya

June 30, 2026

Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Saboda Karya Dokokin Jarabawa ‎

June 30, 2026

NWUK Expels 34 Students Over Examination Malpractice

June 30, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.