Close Menu
  • Shafin Farko
  • Labarai
  • Ilimi
  • Lafiya
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Wasu
    • Nishadi
    • Ra’ayi
    • Sauyin Yanayi
  • English
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Shafin Farko
  • Labarai

    Aikin Yi, Ilimi da Ƙarfafa Mata: Abubuwan da Dr Muhammad Hamisu UK Ya Sa a Gaba ‎ ‎

    October 13, 2026

    Rasuwar Ugboaja Ta Bar Babban Gibi A Ƙungiyar Ƙwadago — Abbas

    August 27, 2026

    “Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

    July 11, 2026

    NWUK Expels 34 Students Over Examination Malpractice

    June 30, 2026

    NDLEA Ta Kone Tan 12.2 Na Miyagun Ƙwayoyi a Kano, Ta Kama Mutum 

    June 29, 2026
  • Ilimi

    Jami’ar Northwest Ta Kano Ta Karɓi Tawagar NUC Domin Tantance Shirin Karatun Tattalin Arziki, A Ci Gaba Da Ayyukan Tantancewa

    November 2, 2026

    Aikin Yi, Ilimi da Ƙarfafa Mata: Abubuwan da Dr Muhammad Hamisu UK Ya Sa a Gaba ‎ ‎

    October 13, 2026

    Rasuwar Ugboaja Ta Bar Babban Gibi A Ƙungiyar Ƙwadago — Abbas

    August 27, 2026

    Allah Ya yi wa Alhaji Sani Gwarzo, wanda aka fi sani da “Tumbuleke”, rasuwa.

    August 11, 2026

    Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

    July 22, 2026
  • Lafiya

    Shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da yunƙurin juyin mulki a watan Oktoban bara

    January 27, 2026

    Kwalara ta kashe mutane 4,778 a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024

    October 6, 2025

    Yadda talauci ke ingiza mutane sayar da ƙodarsu a Nijeriya

    September 29, 2025

    Allurar rigakafin ƙwayar cutar HIV da ake yi kan kudi N70,000 ta sanya a zukatan yan Nijeriya

    September 29, 2025

    Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya

    September 27, 2025
  • Siyasa

    Kwankwaso da Obi sun koma jam’iyyar NDC

    May 3, 2026

    HARIN FARM CENTRE: Kada A Bari Rikicin Siyasa Ya Lalata Tattalin Arzikin Kano — Abbas Ibrahim

    April 29, 2026

    Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

    April 15, 2026

    Tsagin ADC ƙarƙashin David Mark ya kori Nafiu Bala da wasu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

    April 15, 2026

    Gawuna da Kwankwaso sun hade

    March 31, 2026
  • Tsaro

    Rundunar ’Yan Sandan Kano Ta Tattauna Da Matasa Kan Zaman Lafiya A Lokacin Zaɓe

    November 3, 2026

    Kano Police Engage Youths, Civil Society Groups on Peaceful Elections

    November 3, 2026

    Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

    April 25, 2026

    Dole Najeriya ta samu tsaro – Babban hafsan tsaro

    April 20, 2026

    Mutane sama da 50 sun rasu a kuskuren harin sojin sama a kasuwa

    April 13, 2026
  • Wasanni
  • Wasu
    • Nishadi
    • Ra’ayi
    • Sauyin Yanayi
  • English
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home»Uncategorized»Wakilan SNB Sun Shaida Tarihi Da Kyawawan Wuraren Yawon Buɗe Ido A Bauchi
Uncategorized

Wakilan SNB Sun Shaida Tarihi Da Kyawawan Wuraren Yawon Buɗe Ido A Bauchi

October 2, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
20261002 105157 COLLAGE

DAGA ABBAS IBRAHIM

Kusan mutane 200 daga cikin ƙwararrun masu yaɗa labarai a Najeriya sun samu damar ziyartar wasu muhimman wuraren tarihi da yawon buɗe ido a Jihar Bauchi, yayin taron shekara-shekara na uku na Ƙungiyar Kwarraru Masu yada Labarai ta Najeriya, Society of Nigerian Broadcasters SNB.

An gudanar da taron daga ranar 27 zuwa 30 ga Satumba, 2026, inda baya ga tattauna batutuwan da suka shafi aikin yaɗa labarai, mahalarta suka samu damar zagaya wasu wuraren tarihi da yawon buɗe ido da suka shahara a jihar.

A yayin rangadin, tawagar SNB ta ziyarci gidan baje kolin kayayyakin tarihi na Hukumar Kula da Gidajen Tarihi da Abubuwan Tarihi ta Ƙasa (NCMM), inda aka nuna musu wasu kayayyakin marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa, Firayim Ministan Najeriya na farko, wanda ya fito daga Jihar Bauchi.

Daga cikin kayayyakin da aka nuna akwai gadonsa, kujerarsa, rediyo, takobi, huluna da rawuna. Haka kuma, an nuna wata talabijin ɗin kamfanin Sony da aka ce Sarauniya Elizabeth ta bai wa Tafawa Balewa kyauta.

Bayan haka, tawagar ta ziyarci kabarin Tafawa Balewa, wanda ya rasu a ranar 15 ga Janairu, 1966, a lokacin da Najeriya ke fuskantar babban rikicin siyasa da ya biyo bayan juyin mulkin soja na farko a ƙasar.

Daga wuraren tarihi, mahalarta taron suka zarce zuwa Yankari Game Reserve, ƙarƙashin jagorancin Shugaban SNB, Farfesa Umar A. Pate, tare da rakiyar Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Bauchi, Alhaji Usman Shehu Usman.

Jami’an ’yan sanda sun samar da tsaro ga tawagar yayin tafiyar, inda ASP Kabiru ya jagoranci jami’an da suka kula da tsaron mahalarta.

Bayan isa Yankari, an yi wa baƙin bayani kan dokokin tsaro da ka’idojin da ya kamata su bi kafin shiga wuraren yawon buɗe ido.

Mahalarta sun samu damar ganin sanannen ruwan zafi na Yankari, wani ƙaramin gidan adana kayayyakin namun daji, da kuma birai da ke yawo cikin ’yanci a muhallinsu.

Birai sun ja hankalin mahalarta sosai, musamman yadda suke kusantar mutane tare da ƙoƙarin kwace abinci daga hannun wasu baƙi.

Ziyarar ta kuma ba mahalarta damar ganin wasu ayyukan da ake gudanarwa domin inganta Yankari, ciki har da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana, gyaran gidan baƙi na VIP, da kuma sauran abubuwan more rayuwa da suka haɗa da masallaci, gidan cin abinci da shagon sayar da kayayyakin yawon buɗe ido.

Wasu daga cikin mahalarta sun bayyana sha’awarsu ta sake dawowa Yankari domin yin dogon zama, abin da ke nuna irin damar da wurin ke da ita wajen jawo masu yawon buɗe ido daga sassan Najeriya da ƙasashen waje.

Sai dai masana harkar yawon buɗe ido na ganin cewa bunƙasar irin waɗannan wurare na buƙatar ƙarin saka jari, ingantaccen tsaro, hanyoyi masu kyau, ƙarin masauki da kuma tallata wuraren yadda ya kamata.

A wani ɓangare na taron, Gwamnan Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad, ya shirya liyafar cin abinci ga mahalarta a Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi.

A yayin liyafar, an gabatar da wasannin al’adu, inda mahalarta suka samu damar ganin wasu daga cikin al’adu da tarihi na mutanen jihar.

Babbar Daraktar Cibiyar Wole Soyinka ta Aikin Jarida Mai Bincike, Dr Motunrayo Akala, ta bayyana farin cikinta da sake ziyartar Bauchi, inda ta ce ta taɓa zama a jihar a matsayin ’yar yi wa ƙasa hidima kimanin shekaru 21 da suka gabata.

Ta ce irin tarbar da ta samu a lokacin ya sa ziyararta ta yanzu ta kasance kamar komawa gida.

A yayin taron, an kuma tattauna batun walwalar ma’aikatan kafafen yaɗa labarai da kuma yanayin aikin jarida a jihar.

Gwamnan ya bayyana matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka kan batun ma’aikatan wucin gadi a kafafen yaɗa labarai, lamarin da ya samu kulawar mahalarta taron.

Ga ’yan jarida da masu Yaɗa labarai, batun tsaron aikin ma’aikata na da muhimmiyar alaƙa da ingancin aikin jarida da kuma damar kafafen yaɗa labarai na gudanar da ayyukansu cikin ’yanci da ƙwarewa.

Ziyarar SNB ta kuma sake bayyana irin damar da Jihar Bauchi ke da ita a fannin yawon buɗe ido, musamman daga tarihin Tafawa Balewa zuwa namun daji da ruwan zafi na Yankari.

Mahalarta taron sun tashi daga Bauchi da sabbin abubuwa game da tarihi, al’adu da kyawawan wuraren yawon buɗe ido na jihar, bayan da suka je domin halartar taron ƙwararru na SNB.

Rahoton ya nuna cewa, baya ga kasancewa cibiyar tarihi da al’adu, Bauchi na da damar amfani da wuraren yawon buɗe idonta wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga al’umma.

Abbas Ibrahim writes from Kano and can be reached at abbasibrahim664@gmail.com

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Jam’iyyar Labour Labour Party Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Hana Jam’iyyun Adawa wuraren sanya Allunan Talla 

October 21, 2026

AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano

October 14, 2026

Over 380 Arrested, 230 Convicted in Kano Drug Crackdown — Gov. Yusuf

October 1, 2026

Gwamnatin Kano Za Ta Tallafa Wa duk Wani Yunkurin Da Zai Kawar Da Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi A Jihar 

September 9, 2026

Kano Govt Pledges Support as Recovery Hub Launches Campaign Against Drug Abuse

September 9, 2026

Kotu Ta Yanke Wa Mutane Biyu Daurin Shekaru 9 Kan Bai Wa Yara Kanana Kayan Shaye-shaye

September 8, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202417

Kano Police Engage Youths, Civil Society Groups on Peaceful Elections

November 3, 202612

Wakilan SNB Sun Shaida Tarihi Da Kyawawan Wuraren Yawon Buɗe Ido A Bauchi

October 2, 20269

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20249
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Nishadi

Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin Film ko waka a Kano

By WafsymJanuary 20, 2025

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano dake arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan…

Madrid ko Barca: Wa zai lashe Spanish Super Cup?

January 12, 2025

Barca ta kara rashin nasarar ɗaukaka kara kan yi wa Olmo rijista

December 31, 2024

FA ta dakatar da Mudryk daga buga kwallo – Barcelona ta dauki dan kasar Mali Ibrahim Diarra (17) daga Academia África Foot – FAGEN WASANNI

December 17, 2024
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Shafin Farko
  • Game da Mu
  • Tuntube Mu
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.