Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a zaɓen 2023 Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun koma jam’iyar NDC.
Jiga-jigan adawar sun karɓi katin jam’iyar ne bayan ficewa daga jam’iyar ADC saboda rikice-rikicen shugabanci da suka ce sun dabaibaye ta.
HARIN FARM CENTRE: Kada A Bari Rikicin Siyasa Ya Lalata Tattalin Arzikin Kano — Abbas Ibrahim
Dukkansu sun karɓi katin NDC ne a hedikwatar jam’iyar tare da jagoranta Hon. Seriake Dickson.
Ana ta hasashen cewa jiga-jigan adawar na son yin takarar shugaban ƙasa da mataimaki, inda magoya bayansu suka ƙaddamar da wata tafiya da suka kira da OK Movement.

