Hukumar Zabe ta jihar Kano KANSIEC ta rantsar da Honarabul. Ali Musa Ɗanmaliki, (Hardwoker) a matsayin halartaccen shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano.
Hukumar ta rantsar da Hardwoker, ne a yau Talata, bayan sauke Abdullahi Ghali Basaf daga shugaban karamar hukumar Kumbotso, yayin da aka maye gurbin sa da Ali Musa.
Read also: Rundunar ’Yan Sandan Kano Ta Tattauna Da Matasa Kan Zaman Lafiya A Lokacin Zaɓe
Matatar Ɗangote ta fitar da tan 456,000 na man fetur zuwa wasu ƙasashen Afrika
Read also: Kano Police Engage Youths, Civil Society Groups on Peaceful Elections
Bayan hukuncin babbar kotun jihar Kano na sauke Ghali Abdullahi Basaf daga shugabancin ƙaramar hukumar Kumbotso, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ta mika shedar lashe zaɓe ga Hon. Ali Musa Hardworker.
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Kano, KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya mika shedar a yau Talata a gidan gwamnatin jihar Kano.

