Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎
Afrika

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
FB IMG 1770849624495

A daidai lokacin da ya rage ‘yan kwanaki kaɗan a shiga watan Ramadan mai alfarma, mazauna jihar Kano na fuskantar tashin gwauron zabi na farashin kayan masarufi, musamman waɗanda ake amfani da su wajen shirya buɗa baki.

‎Wani bincike da Daily News 24 ta gudanar a wasu manyan kasuwannin Kano, ciki har da Sheka da Rimi, ya nuna cewa farashin kayayyaki irin su zobo, tsamiya da kayan ƙamshi ya ƙaru da kusan kashi 60 cikin ɗari cikin makonni biyu kacal.

‎NAPTIP Ta Ceto Mata Bakwai Ake Zargin Ana Shirin Safarar Su zuwa Ƙasar Iraki A Kano ‎

‎Wasu ‘yan kasuwa sun danganta karin farashin da yawaitar buƙata a lokacin tunkarar Ramadan, tare da zargin cewa wasu manyan dillalai na ɓoye kaya domin sayar da su da tsada a gaba.

‎Nasiru Muhammad, wani ɗan kasuwa a kasuwar Sheka, ya ce tashin farashin ya fara ne tun kafin watan azumi ya karaso.

‎“Farashi ya bambanta sosai idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Har ma ana sa ran zai ƙara tashi, domin wasu ‘yan kasuwa na ɓoye kaya don su sayar da su da tsada daga baya,” in ji shi.

‎Masu sayayya ma na bayyana damuwa kan yadda farashin kayayyaki ke ƙaruwa cikin gaggawa.

‎Amina Hamza, wata mai sayayya, ta ce farashin zobo ya tashi daga naira 1,200 zuwa naira 2,000 a cikin ɗan lokaci, yayin da ta ce ingancin kayan ma ya ragu.

‎Ta kuma ce farashin citta ya tashi daga naira 12,000 kan rabin kwano zuwa naira 14,000 cikin ƙasa da makonni biyu.

‎A kasuwar Rimi kuwa, wani mai sayar da kayan ƙamshi, Rabi’u Nakaka, ya ce farashin masoro ya tashi daga naira 2,500 zuwa naira 4,000 kan gwangwani ɗaya, yayin da tsamiya ma ta ƙaru sakamakon yawaitar buƙata domin yin kunun tsamiya a watan Ramadan.

‎Duk da cewa wasu ‘yan kasuwa na hasashen yiwuwar farashi ya lafa a tsakiyar watan azumi, sun gargadi cewa boye kaya da dillalai ke yi na iya ƙara tsananta matsin tattalin arziki ga al’umma.

‎Mazauna Kano dai na ci gaba da fatan hukumomi za su dauki matakan da za su rage tashin farashin, domin sauƙaƙa wa jama’a yayin da watan Ramadan ke gabatowa.

Ramadan
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026

Maki shida ne ya rage tsakanin Arsenal da Man City

April 13, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.