Close Menu
  • Shafin Farko
  • Labarai
  • Ilimi
  • Lafiya
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Wasu
    • Nishadi
    • Ra’ayi
    • Sauyin Yanayi
  • English
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Shafin Farko
  • Labarai

    Aikin Yi, Ilimi da Ƙarfafa Mata: Abubuwan da Dr Muhammad Hamisu UK Ya Sa a Gaba ‎ ‎

    October 13, 2026

    Rasuwar Ugboaja Ta Bar Babban Gibi A Ƙungiyar Ƙwadago — Abbas

    August 27, 2026

    “Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

    July 11, 2026

    NWUK Expels 34 Students Over Examination Malpractice

    June 30, 2026

    NDLEA Ta Kone Tan 12.2 Na Miyagun Ƙwayoyi a Kano, Ta Kama Mutum 

    June 29, 2026
  • Ilimi

    Aikin Yi, Ilimi da Ƙarfafa Mata: Abubuwan da Dr Muhammad Hamisu UK Ya Sa a Gaba ‎ ‎

    October 13, 2026

    Rasuwar Ugboaja Ta Bar Babban Gibi A Ƙungiyar Ƙwadago — Abbas

    August 27, 2026

    Allah Ya yi wa Alhaji Sani Gwarzo, wanda aka fi sani da “Tumbuleke”, rasuwa.

    August 11, 2026

    Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

    July 22, 2026

    “Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

    July 11, 2026
  • Lafiya

    Shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da yunƙurin juyin mulki a watan Oktoban bara

    January 27, 2026

    Kwalara ta kashe mutane 4,778 a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024

    October 6, 2025

    Yadda talauci ke ingiza mutane sayar da ƙodarsu a Nijeriya

    September 29, 2025

    Allurar rigakafin ƙwayar cutar HIV da ake yi kan kudi N70,000 ta sanya a zukatan yan Nijeriya

    September 29, 2025

    Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya

    September 27, 2025
  • Siyasa

    Kwankwaso da Obi sun koma jam’iyyar NDC

    May 3, 2026

    HARIN FARM CENTRE: Kada A Bari Rikicin Siyasa Ya Lalata Tattalin Arzikin Kano — Abbas Ibrahim

    April 29, 2026

    Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

    April 15, 2026

    Tsagin ADC ƙarƙashin David Mark ya kori Nafiu Bala da wasu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

    April 15, 2026

    Gawuna da Kwankwaso sun hade

    March 31, 2026
  • Tsaro

    Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

    April 25, 2026

    Dole Najeriya ta samu tsaro – Babban hafsan tsaro

    April 20, 2026

    Mutane sama da 50 sun rasu a kuskuren harin sojin sama a kasuwa

    April 13, 2026

    BINCIKE: An samu karin kashi 543% a yaduwar cutar dajin dake kama nono a Najeriya

    March 4, 2026

    Ƙalubalen da ke gaban sabon Sufeto Janar na ‘yansandan Nijeriya

    February 26, 2026
  • Wasanni
  • Wasu
    • Nishadi
    • Ra’ayi
    • Sauyin Yanayi
  • English
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home»Uncategorized»Kotu Ta Yanke Wa Mutane Biyu Daurin Shekaru 9 Kan Bai Wa Yara Kanana Kayan Shaye-shaye
Uncategorized

Kotu Ta Yanke Wa Mutane Biyu Daurin Shekaru 9 Kan Bai Wa Yara Kanana Kayan Shaye-shaye

September 8, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
1770252958766

Kotu Ta Yanke Wa Mutane Biyu Daurin Shekaru 9 Kan Bai Wa Yara Kanana Kayan Shaye-shaye

 

Kwamitin Hadin Gwiwar Hukumomi na Jihar Kano kan Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Fataucin Haramtattun Abubuwa ya samu nasarar gurfanar da wasu mutane biyu tare da tabbatar da hukuncin dauri shekara Tara (9) a kansu bisa laifin samar da sinadarin solisho da wasu abubuwa masu sanya maye ga yara.

Hukuncin ya zama gargaɗi mai ƙarfi ga duk wanda ke cin gajiyar raunanan yara tare da jefa su cikin haɗarin shan abubuwan maye, cewa za su fuskanci cikakken hukuncin da doka ta tanada.

 

Wadanda aka samu da laifin su ne, Kabiru Isa (Mada) da Usman Hamisu (Mani). Mai Shari’a Muhammad Alhaji Sani na Kotun Majistare mai lamba 44 da ke Gwammaja, Kano, ya yanke musu hukuncin, bayan samunsu da laifukan haɗa baki wajen aikata laifi, kasancewa membobin haramtacciyar ƙungiya da kuma bai wa wasu abubuwa masu sa maye, sabanin tanade tanaden Sashe na 97, 97A da 249 na Kundin Dokokin Penal Code.

 

Kotun ta yanke wa kowannensu hukuncin ɗaurin shekaru 9, ba tare da zaɓin biyan tara ba, inda hukuncin zai gudana a jere.

 

Kotun ta kuma umarci cewa kowace shekara daga cikin hukuncin za a yi ta a matsayin cikakkun watanni 12 na kalanda, ba tare da cire ranakun ƙarshen mako ba, wanda ke nufin wadanda aka yanke wa hukuncin za su cika wa’adin hukuncin da kotu ta yanke musu.

 

Hukuncin ya biyo bayan wani bincike mai zurfi da Kwamitin Hadin Gwiwar Hukumomi na Jahar Kano kan Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Fataucin Haramtattun Abubuwa ya gudanar karkashin jagorancin Shugabansa, Barrista Muhuyi Magaji, dangane da yadda yara marasa galihu a titunan Race Course da ke Kano ke fuskantar amfani da abubuwan maye.

 

Lamarin ya samo asali ne bayan ceto yara kanana guda 43, wadanda basu balaga ba, daga yankin Race Course. Wasu daga cikin yaran ‘yan asalin Jihar Kano ne, yayin da wasu suka fito daga wasu jihohin kasar nan, inda suka tsinci kansu cikin mawuyacin halin rayuwar titi.

 

Binciken da Kwamitin ya gudanar ya gano wani abin damuwa, inda ake bai wa wasu daga cikin yaran da ke yin sana’ar Baban bola a tituna sinadarin solisho mai sa maye da sauran abubuwa masu cutarwa maimakon a biya su da hakkin aikinsu. Wannan dabi’a ta jefa yaran cikin haɗarin shan abubuwan maye tare da kara tsananta raunin da suke ciki.

 

Kamawa, gurfanarwa da kuma hukunta mutanen biyu wani muhimmin mataki ne na tabbatar da doka da Kwamitin ya dauka, wanda kuma ya kara tabbatar da kudurinsa na rushe duk wasu hanyoyi da ayyukan da ke cin gajiyar raunanan yara tare da jefa matasa cikin shan miyagun kwayoyi.

 

Kwamitin ya bayyana karara cewa tabbatar da doka da hukunta masu karya ta na daga cikin manyan abubuwan da ke cikin aikinsa. Duk wani mutum ko kungiyar da ke samar da abubuwa masu sa maye ga yara, ko ke cin gajiyar raunanan matasa, ko kuma ke karfafa shan miyagun kwayoyi, za a gano shi, a bincike shi, a kama shi tare da gurfanar da shi bisa tanadin doka.

 

Sai dai aikin Kwamitin bai tsaya kawai kan kamawa da gurfanarwa ba.

 

Ceto yaran 43 wani bangare ne na babban kudurin Kwamitin na fitar da matasa masu rauni 10,000 daga tituna, musamman wadanda ke fuskantar haɗarin shan miyagun kwayoyi da sauran munanan abubuwa, tare da samar musu da wata ingantacciyar hanya ta samun sauyi da kyakkyawar makoma.

 

A karkashin wannan shiri, za a fitar da matasa masu rauni daga muhallin da ke jefa su cikin hadari, sannan a gudanar da binciken lafiyarsu da halin da suke ciki. Wadanda ke bukatar magani za a ba su kulawar da ta dace, yayin da sauran kuma za a tallafa musu ta hanyar gyaran hali, koyon sana’o’i da kuma sake shigar da su cikin al’umma.

 

Manufar ba wai kawai fitar da matasa daga tituna ba ce, amma samar musu da damar sake gina rayuwarsu cikin mutunci, koyon sana’o’i masu amfani da kuma zama mutane masu amfani ga al’ummominsu.

 

Da yake magana kan hukuncin da kuma wannan babban shiri, Shugaban Kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji, ya ce Kwamitin zai ci gaba da gudanar da aikinsa cikin tsaurin doka, tare da hada matakan tabbatar da doka da rigakafi, jinya, gyaran hali da sake shigar da mutane cikin al’umma.

 

Ya jaddada cewa yara da matasan da suka fada cikin hadarin shan miyagun kwayoyi bai kamata a rika kallonsu ta fuskar hukunci kawai ba, sai dai a kuma ba su kariya tare da damar samun sauki da sake gina rayuwarsu.

 

A lokaci guda, ya yi gargadi cewa duk wanda ke cin gajiyar raunin yara da matasa domin amfanin kansa ba zai tsira daga fuskantar hukunci ba.

 

Kwamitin ya kuma yi kira ga iyaye, shugabannin al’umma, hukumomin gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su kara kaimi wajen kare yara da matasa daga illolin shan miyagun kwayoyi.

 

Kwamitin ya jaddada cewa yaki da shan miyagun kwayoyi da fataucin haramtattun abubuwa ba aikin hukumomin gwamnati kadai ba ne. Yaki ne na kowa wanda ke bukatar sa ido, hadin kai da cikakken jajircewar iyaye, al’ummomi, hukumomi da dukkanin ‘yan kasa.

 

Sakon da wannan hukunci ya aika a bayyane yake: bai kamata tituna su zama wuraren da ake cin gajiyar yara ba, kuma duk wanda ke samar da abubuwa masu sa maye ga matasa masu rauni za a bi diddiginsa, a kama shi, a gurfanar da shi kuma a hukunta shi bisa doka.

 

Yayin da masu aikata irin wadannan laifuka za su fuskanci sakamakon ayyukansu, Kwamitin zai ci gaba da bai wa yara da matasa masu rauni kariya, jinya, gyaran hali, koyon sana’o’i da kuma sabuwar damar gina rayuwa mai amfani tare da bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Jam’iyyar Labour Labour Party Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Hana Jam’iyyun Adawa wuraren sanya Allunan Talla 

October 21, 2026

AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano

October 14, 2026

Wakilan SNB Sun Shaida Tarihi Da Kyawawan Wuraren Yawon Buɗe Ido A Bauchi

October 2, 2026

Over 380 Arrested, 230 Convicted in Kano Drug Crackdown — Gov. Yusuf

October 1, 2026

Gwamnatin Kano Za Ta Tallafa Wa duk Wani Yunkurin Da Zai Kawar Da Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi A Jihar 

September 9, 2026

Kano Govt Pledges Support as Recovery Hub Launches Campaign Against Drug Abuse

September 9, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202417

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20249

Wakilan SNB Sun Shaida Tarihi Da Kyawawan Wuraren Yawon Buɗe Ido A Bauchi

October 2, 20267

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Nishadi

Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin Film ko waka a Kano

By WafsymJanuary 20, 2025

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano dake arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan…

Madrid ko Barca: Wa zai lashe Spanish Super Cup?

January 12, 2025

Barca ta kara rashin nasarar ɗaukaka kara kan yi wa Olmo rijista

December 31, 2024

FA ta dakatar da Mudryk daga buga kwallo – Barcelona ta dauki dan kasar Mali Ibrahim Diarra (17) daga Academia África Foot – FAGEN WASANNI

December 17, 2024
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Shafin Farko
  • Game da Mu
  • Tuntube Mu
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.