Close Menu
  • Shafin Farko
  • Labarai
  • Ilimi
  • Lafiya
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Wasu
    • Nishadi
    • Ra’ayi
    • Sauyin Yanayi
  • English
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Shafin Farko
  • Labarai

    Aikin Yi, Ilimi da Ƙarfafa Mata: Abubuwan da Dr Muhammad Hamisu UK Ya Sa a Gaba ‎ ‎

    October 13, 2026

    Rasuwar Ugboaja Ta Bar Babban Gibi A Ƙungiyar Ƙwadago — Abbas

    August 27, 2026

    “Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

    July 11, 2026

    NWUK Expels 34 Students Over Examination Malpractice

    June 30, 2026

    NDLEA Ta Kone Tan 12.2 Na Miyagun Ƙwayoyi a Kano, Ta Kama Mutum 

    June 29, 2026
  • Ilimi

    Aikin Yi, Ilimi da Ƙarfafa Mata: Abubuwan da Dr Muhammad Hamisu UK Ya Sa a Gaba ‎ ‎

    October 13, 2026

    Rasuwar Ugboaja Ta Bar Babban Gibi A Ƙungiyar Ƙwadago — Abbas

    August 27, 2026

    Allah Ya yi wa Alhaji Sani Gwarzo, wanda aka fi sani da “Tumbuleke”, rasuwa.

    August 11, 2026

    Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

    July 22, 2026

    “Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

    July 11, 2026
  • Lafiya

    Shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da yunƙurin juyin mulki a watan Oktoban bara

    January 27, 2026

    Kwalara ta kashe mutane 4,778 a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024

    October 6, 2025

    Yadda talauci ke ingiza mutane sayar da ƙodarsu a Nijeriya

    September 29, 2025

    Allurar rigakafin ƙwayar cutar HIV da ake yi kan kudi N70,000 ta sanya a zukatan yan Nijeriya

    September 29, 2025

    Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya

    September 27, 2025
  • Siyasa

    Kwankwaso da Obi sun koma jam’iyyar NDC

    May 3, 2026

    HARIN FARM CENTRE: Kada A Bari Rikicin Siyasa Ya Lalata Tattalin Arzikin Kano — Abbas Ibrahim

    April 29, 2026

    Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

    April 15, 2026

    Tsagin ADC ƙarƙashin David Mark ya kori Nafiu Bala da wasu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

    April 15, 2026

    Gawuna da Kwankwaso sun hade

    March 31, 2026
  • Tsaro

    Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

    April 25, 2026

    Dole Najeriya ta samu tsaro – Babban hafsan tsaro

    April 20, 2026

    Mutane sama da 50 sun rasu a kuskuren harin sojin sama a kasuwa

    April 13, 2026

    BINCIKE: An samu karin kashi 543% a yaduwar cutar dajin dake kama nono a Najeriya

    March 4, 2026

    Ƙalubalen da ke gaban sabon Sufeto Janar na ‘yansandan Nijeriya

    February 26, 2026
  • Wasanni
  • Wasu
    • Nishadi
    • Ra’ayi
    • Sauyin Yanayi
  • English
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home»Uncategorized»RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki
Uncategorized

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260308 WA0030

‎Rundunar Kano Neighbourhood Watch Security Corps, wadda gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin tallafawa hukumomin tsaro a matakin al’umma, ta fara samun tasiri duk da cewa ba ta jima da fara aiki ba.

‎Rundunar ta fara aiki a hukumance a ranar 23 ga Disamba, 2025, kuma a cikin watanni uku da suka gabata, jami’anta sun fara taka rawa a fannoni kamar tattara bayanan sirri, dakile yunƙurin garkuwa da mutane, kai ɗauki lokacin gobara da kuma taimakawa  wajen gano masu aikata laifuka.

‎Farashin litar man fetur ya zarce naira dubu 1 a sassan Najeriya

‎Sai dai duk da wannan ci gaba, wasu daga cikin jama’a da masana na ganin cewa har yanzu rundunar na bukatar ƙarin tsari, kulawa da kuma fadada ayyukanta domin cimma burin da aka kafa ta a kai.

‎Babban Kwamandan Rundunar, Laftanar Kanal Aminu Yusuf Abdulmalik mai ritaya, ya bayyana cewa a matakin farko rundunar ta fi mayar da hankali ne kan gina tsarin aiki, tsarin tura jami’anta domin fara aiki a wasu kananan hukumomi.

‎A cewarsa, rundunar na cikin wani mataki da ya kira “matakin ƙarfafa tsari”, inda ake ƙara inganta ayyukan rundunar tare da fadada ayyukanta a cikin al’umma.

‎“Mun fara ganin wasu alamun ƙarfafawa musamman wajen tattara bayanan sirri daga cikin al’umma da kuma saurin amsa kiran gaggawa,” in ji shi.

‎Shugaban rundunar ya ce jami’an sun fara aiki tare da sauran hukumomin tsaro ta hanyar sintiri da kuma sa ido kan al’amuran tsaro, domin gano matsaloli tun kafin su tsananta. ‎

A cewarsa, sabuwar rundunar ta fara aiki da taimakawa wajen wasu ayyukan tsaro a sassan jihar, Yana mai bayar da misali, na yadda jami’an rundunar suka ba da gudummawa wajen fuskantar matsalolin tsaro da suka shafi garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga a kananan hukumomin Bagwai, Shanono da Gwarzo.

‎A Karamar Hukumar Dambatta ma, jami’an rundunar sun taimaka wajen dakile wani yunƙurin garkuwa da wani mutum, sannan suka ba da agaji lokacin da gobara ta tashi a Kasuwar Singa.

‎Haka kuma a unguwar Dorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale, jami’an rundunar sun taimaka wa hukumomi wajen gudanar da bincike kan wani zargi na kisan kai.

‎Rundunar Neighbourhood Watch ta Kano na aiki ne bisa wani tsari da aka shimfiɗa domin tabbatar da cewa ayyukan tsaro sun kai ga al’umma, t‎sarin fa ya haɗa da babbar hedikwatar rundunar a matakin jiha, rundunonin sassa guda biyar, kwamandojin kananan hukumomi da kuma rukunin jami’ai a matakin unguwanni.

‎Shugaban rundunar ya ce kusantar da jami’an tsaro ga al’umma na daga cikin muhimman ginshiƙan nasarar wannan shiri.

‎“Yawancin barazanar tsaro na farawa ne daga cikin al’umma. Don haka, idan jami’ai suna kusa da al’umma, lallai hakan zai taimaka wajen gano matsaloli tun da wuri,” in ji Abdulmalik.

‎Game da yiwuwar amfani da rundunar ta hanyar siyasa ko cin zarafi, shugabannin rundunar sun ce an gudanar da daukar ma’aikata da nade-naden mukamai ne bisa ƙa’idojin ƙwarewa da gaskiya.

‎Sun ce an yi la’akari da abubuwa kamar haka: ilimi, gaskiya, kwarewar jagoranci da kuma lafiyar jiki da ta kwakwalwa wajen daukar jami’ai.

‎Rundunar ta kuma kafa dokokin aiki da tsarin ladabtarwa, tare da horar da jami’anta kan haƙƙin bil’adama da kuma yadda za su yi amfani da ƙarfi cikin doka. ‎Haka kuma, Hukumar ba za ta amincewa duk wata manufa ta cin hanci ko cin zarafi ko tsare mutane ba bisa ka’ida ba.

Ya ce, ‎Jama’a za su iya kai korafe korafensu zuwa ofisoshin kananan hukumomi ko kuma ta January tura sako ta lambobin waya na hedikwatar rundunar da ke harabar KNARDA a kan titin Hadejia.

‎Duk da irin wannan nasarorin farko da Hukumar ta samu, shugaban rundunar ya amince cewa har yanzu ayyukan hukumar bai kai ga wasu sassan jihar ba.

‎A cewarsa, hakan na da nasaba da aikin daukar sabbin jami’ai da kuma horo da ake gudanarwa tare da hadin gwiwar Hukumar Ma’aikatan Jiha.

‎Sai dai ya ce bayan kammala wadannan matakai, ana sa ran jama’a za su fara ganin karin jami’an rundunar a dukkan unguwanni.

A tattaunawa da wani ‎Masani kan manufofin gwamnati, Malam Tijjani Sarki, ya ce rundunar ta na da amfani, kuma za ta iya taimakawa sosai wajen inganta tsaro a matakin al’umma idan aka tafiyar da ita cikin ƙwarewa da adalci.

‎Sai dai ya jaddada muhimmancin ci gaba da sa ido da kulawa domin kauce wa yiwuwar amfani da iko ta hanyar bai kamata ba.

Ana ta bangaren, Hajiya Khadija Naseer, wata malamar makarantar sakandare, ta ce har yanzu lokaci bai yi ba ta yadda za a iya tantance tasirin rundunar gaba ɗaya, kasancewar sabuwa ce har yanzu.

‎Shi kuwa wani dan kasuwa a Kasuwar Kwari, Yasir Sani Abdullahi ‎ya buƙaci a ƙara yawan jami’an Kano Neighbourhood Watch Corps domin ƙarfafa tsaro a faɗin Jihar Kano.

‎Ya ce duk da cewa ɗaukar jami’ai 2,000 da gwamnatin jihar ta yi wani mataki ne mai kyau, amma adadin na iya zama bai wadatar ba idan aka yi la’akari da yawan al’ummar da ke rayuwa a cikin jihar da kuma faɗin yankunan da suke buƙatar kulawar tsaro.

‎Abdullahi ya bayyana cewa domin tabbatar da ingantaccen tsaro a matakin al’umma, ya kamata a ƙara yawan jami’an zuwa akalla 10,000, domin su samu damar isa yankuna da dama na birane da karkara.

‎Ya ƙara da cewa tsaro na da matuƙar muhimmanci ga zaman lafiya da ci gaban al’ummar Jihar Kano, yana mai jaddada cewa ƙarfafa irin wannan tsarin tsaro na cikin gida zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

‎Shugabannin rundunar sun ce a halin yanzu abubuwan da suka fi mayar da hankali a kai sun haɗa da kammala tura jami’ai a dukkan unguwanni, ƙarfafa ladabi da bin doka, da kuma ƙara haɗin gwiwa da al’umma, yayin da al’umma ke fatan an gudanar da Hukumar ta hanyar da ya kamata, ba tare da amfani da ita ba wajen muzgunawa al’umma ba.

Kano Neighbourhood
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Jam’iyyar Labour Labour Party Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Hana Jam’iyyun Adawa wuraren sanya Allunan Talla 

October 21, 2026

AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano

October 14, 2026

Wakilan SNB Sun Shaida Tarihi Da Kyawawan Wuraren Yawon Buɗe Ido A Bauchi

October 2, 2026

Over 380 Arrested, 230 Convicted in Kano Drug Crackdown — Gov. Yusuf

October 1, 2026

Gwamnatin Kano Za Ta Tallafa Wa duk Wani Yunkurin Da Zai Kawar Da Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi A Jihar 

September 9, 2026

Kano Govt Pledges Support as Recovery Hub Launches Campaign Against Drug Abuse

September 9, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202417

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20249

Wakilan SNB Sun Shaida Tarihi Da Kyawawan Wuraren Yawon Buɗe Ido A Bauchi

October 2, 20267

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Nishadi

Hukumar tace fina-finai ta haramtawa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin Film ko waka a Kano

By WafsymJanuary 20, 2025

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano dake arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan…

Madrid ko Barca: Wa zai lashe Spanish Super Cup?

January 12, 2025

Barca ta kara rashin nasarar ɗaukaka kara kan yi wa Olmo rijista

December 31, 2024

FA ta dakatar da Mudryk daga buga kwallo – Barcelona ta dauki dan kasar Mali Ibrahim Diarra (17) daga Academia África Foot – FAGEN WASANNI

December 17, 2024
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Shafin Farko
  • Game da Mu
  • Tuntube Mu
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.