Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Kwamitin Gudanarwar Jami’ar Northwest, dake nan Kano, bisa nada Shugabar Jami’ar (Vice Chancellor) cikakkiya bayan bin sahihin tsari mai tsawo, adalci da gaskiya.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.
Bash M Bash: Lalacewar Masana’antu Na Jefa Tattalin Arzikin Kano Cikin Barazana
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin zaman Majalisar Zartarwa karo na 35, inda Shugaban Kwamitin Gudanarwar jami’ar (Pro-Chancellor) ya jagoranci mambobin kwamitin da shugabannin jami’ar wajen kai ziyarar girmamawa domin gabatar da Farfesa Amina Salihi Bayero a hukumance a matsayin sabuwar Shugabar Jami’ar.
Farfesa Amina Bayero ita ce Shugabar Jami’a mace ta farko a tarihin jami’ar, wadda ta ta faro tun daga tushe kasancewarta daga cikin ma’aikatan koyarwa na farko tun kafuwar jami’ar mallakin jiha.
Gwamna Yusuf ya shawarci sabuwar Shugabar Jami’ar da ta gudanar da aikinta da himma da gaskiya, tare da yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin bunƙasa ingancin ilimi a tsawon wa’adin mulkinta na shekaru biyar.
Ya kuma tabbatar wa sabuwar shugabar jami’ar cikakken goyon bayan gwamnatin jiha wajen magance ƙalubalen da jami’ar ke fuskanta.
Gwamnan ya sanar da cewa za a biya dukkan bashin alawus-alawus na koyarwa (Earned Academic Allowances – EAA) da ake bin ma’aikatan jami’ar kafin ƙarshen watan Disamba.
Haka zalika, ya ba da umarni ga Kwamishinan ma’aikatar Kasa da Tsara Birane da ya tantance dukkan filayen jami’ar tare da soke duk wani fili da aka bada shi ba bisa ka’ida ba a lokacin gwamnatin da ta gabata.
Gwamna Yusuf ya nuna godiya bisa ziyarar da aka kai masa, tare da jaddada bukatar da gwamnatin jiha ke da shi na ganin an samu ingantaccen ci gaban ilimi da bunƙasar jami’ar ƙarƙashin sabon shugabanci.
Tun da farko, Shugaban Kwamitin Gudanarwar jami’ar, Farfesa Hafiz Abubakar, ya bayyana cewa zaɓen cikakkiyar Shugabar Jami’ar ya ɗauki tsawon watanni goma, kuma Kwamitin Gudanarwar ya amince da sakamakon baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa nadin Shugabar Jami’a mace ta farko a jami’ar ya samu karɓuwa sosai daga al’umma.
A nata jawabin, Farfesa Amina Salihi Bayero ta gode wa Allah bisa wannan dama da aka ba ta, tare da alƙawarin sadaukar da kanta gaba ɗaya wajen aiwatar da amanar da aka ɗora mata.
Ta kuma gabatar da tsare-tsare guda 14 da ke da nufin sake farfaɗo da jami’ar domin samun ingantaccen ci gaban ilimi da na gudanarwa.

