Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa duk wanda ke son tsayawa takara ko samun mukamin siyasa a Najeriya, abin da ake buƙata kawai shi ne takardar shaidar kammala makarantar sakandare.
Shehu Sani ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai, inda ya ce tsarin doka a Najeriya bai tilasta sai mutum yana da manyan takardun karatu kafin shiga siyasa ba.
NDLEA ta kama tarin ƙwayoyi da ake shirin safararsu zuwa Birtaniya
A cewarsa, “Doka ta bayyana a fili cewa takardar shaidar sakandare ta isa mutum ya tsaya takara ko ya samu mukamin siyasa. Abin da ake bukata shi ne kwarewa, hangen nesa, da gaskiya wajen mulki — ba sai mutum yana da digiri uku ba.”
Ya ƙara da cewa a wasu lokuta, masu digiri da dama ba su da ikon gudanar da shugabanci yadda ya kamata, yayin da wasu masu ilimi mai sauƙi ke da nagartar jagoranci da fahimtar matsalolin jama’a.
Shehu Sani ya yi nuni da cewa abin da ke da muhimmanci shi ne mutum ya kasance mai kishin ƙasa da hangen ci gaba, ba wai takardun karatu kaɗai ba.
Maganganunsa sun jawo muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu ke goyon bayansa suna cewa ilimi ba shi ne auna nagartar shugaba ba, yayin da wasu ke cewa Najeriya na bukatar shugabanni masu zurfin ilimi da hangen nesa domin magance matsalolin da ake fuskanta

