Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sunayen mutane biyu zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni a cikin majalisar zartarwar jiharsa.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.
Wadanda Aka Tura Sunayen su ne
1. Barista Abdulkarim Kabir Maude (SAN designate)
Barista Maude, dan asalin karamar hukumar Minjibir, mai shekaru 40, ana sa ran zai karɓi kambun babban lauya na ƙasa (SAN) gobe Litinin a gaban Kotun Koli.
Ya kammala karatunsa na farko a fannin lauya daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, sannan ya samu digiri na biyu a fannoni biyu — International Economic Law daga Maryam Abacha American University of Niger da Business Commercial Law daga Jami’ar Bayero Kano.
Barista Maude ya shafe sama da shekaru 10 yana aiki a fannoni daban-daban na lauya, ciki har da shari’a, harkokin kasuwanci da kula da kadarori. Shi memba ne na Kungiyar Lauyoyin Najeriya (Nigerian Bar Association) da kuma Chartered Institute of Arbitrators of Nigeria.
2. Dr. Aliyu Isa Aliyu
Dr. Aliyu, mai shekaru 41, kwararre ne a fannin lissafi kuma mai shirin zama Farfesa. Ya karanci digirinsa na farko a Jami’ar Bayero Kano, ya samu digiri na biyu (Masters) daga Jordan University of Science and Technology, sannan ya yi digirin digirgir (Ph.D) a Firat University, Turkiyya.
Ya fara aikin koyarwa a Jami’ar Tarayya Dutse a shekarar 2014 kafin daga bisani ya koma North West University, Kano, inda yake matsayin Associate Professor. Haka kuma ya halarci horaswa a kasashen China da Cyprus.
Tun shekarar 2023, Dr. Aliyu yana rike da mukamin Babban Mai Kidayar Jama’a kuma Kakakin Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano. Shi ne daya daga cikin daliban da suka ci gajiyar tallafin karatun waje na Kwankwasiyya, sannan ya taba rike mukamin sakataren kudi na jam’iyyar NNPP a jihar.
Sabon Solicitor-General
A wani bangare na sanarwar, Gwamna Yusuf ya kuma amince da nadin Barista Salisu Muhammad Tahir a matsayin sabon Solicitor-General kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano.
Kafin wannan nadin, Barista Tahir ya kasance Daraktan Mai Shigar da Kara (Public Prosecution) a ma’aikatar, inda ya yi fice wajen gudanar da ayyukansa.
An umarci shugaban ma’aikata da ya tabbatar da kammala dukkan matakan gudanarwa domin sabon lauya ya fara aiki daga Litinin, 29 ga Satumba, 2025.
“Za Mu Ci Gaba da Zabar Matasa Masu Kwarewa” – Gwamna Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirinsa na ci gaba da zabar matasa masu basira, kwarewa da gaskiya domin kara inganta aikin gwamnati da samar da nagartaccen shugabanci a jihar.
“Jihar Kano tana bukatar sabbin tunani da sabbin dabaru wajen gudanar da mulki. Wannan shi ne dalilin da ya sa muke bai wa matasa damar taka muhimmiyar rawa a gwamnati,” in ji Gwamna Yusuf.

