Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Daga 2025 Najeriya zata fara hako gangar mai miliyan 3 a kowace rana – Heineken Lokpobiri
Afrika

Daga 2025 Najeriya zata fara hako gangar mai miliyan 3 a kowace rana – Heineken Lokpobiri

December 31, 2024
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn

Gwamnatin Nijeriya ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ɓarayin man fetur a yankin Neja Delta a yayin da take shirin fitar da gangar mai miliyan 3 a kowace rana a shekarar 2025.

Nijeriya wadda ke cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen fitar da ɗanyen fetur a Afirka, ta na samun yawancin kuɗin shigarta daga mai, kuma tana samun fiye da kashi 90 na kuɗaɗen ƙasashen waje daga sayar da man fetur, amma tana fama da ɓarayin mai.

A yayin da gwamnatin ƙasar ta yi ƙiyasin fitar da ganga miliyan 2.06 ta man fetur a kasafin kuɗinta na shekara mai zuwa, a zahiri fetur ɗin da take fitarwa bai wuce ganga miliyan 1.8 a kowace rana ba, a cewar alƙaluman da hukumomi suka fitar.

Ma’aikatar man fetur da rundunar sojin sama ta Nijeriya sun ƙaddamar da yaƙi da ɓarayin danyen fetur, mai suna Delta Sanity a shekarar da ta wuce.

Babban Hafsan sojin saman ƙasar Emmanuel Ogalla ya ce yanzu shiri na OPDS ya shiga zango na biyu, inda za su yi amfani da jirage marasa matuƙa da helikwafta da ƙarin jami’an leƙen asiri wajen ganin sun rage matsalar, inda suke sa rai za a riƙa fitar da ɗanyen mai da ya kai ganga miliyan uku a kowace rana.

“Idan ka dubi yadda lamura suke a bara, lokacin da muka ƙaddamar da wannan shiri, muna samun gangar ɗanyen fetur miliyan 1.4 kowace rana. Yanzu ya ƙaru zuwa ganga miliyan 1.8.

“Na yi amanna cewa idan muka kammala ɗaukar wadannan matakai, za mu cim ma manufarmu ko ma mu haura ƙiyasin da muka yi,” a cewar Ogalla a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata bayan ya ƙaddamar da sabon shirin yaƙi da ɓarayin ɗanyen man fetur a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas.

Ƙaramin Ministan Harkokin Man Fetur Heineken Lokpobiri ya ce adadin ɗanyen fetur ɗin da Nijeriya take fitarwa da kaɗan ya wuce ganga miliyan 1 a kowace rana lokacin da ya soma aiki a watan Agustan 2023.

“Burinmu shi ne mu riƙa fitar da ganga miliyan 3 a kowace rana daga yanzu zuwa shekarar 2025 kuma muna da ƙwarin gwiwa cewa ƙaddamar da yaƙi da ɓarayin mai da muka yi a zango na biyu, wato OPDS zai taka muhimmiyar rawa” Inji Heineken

Featured
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Yawan Al’umma Na Iya Tsananta Matsalar Tsaro a Nijeriya-Bankin Duniya

October 20, 2025

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

October 20, 2025

Kano: KIRS Ta Fitar Da Sabon Tsarin Biyan Haraji Ta Hanyar Fasahar Zamani

October 6, 2025

Takardar Sakandire Ta Isa Bayar Da Damar Rike Mukamin Siyasa — Shehu Sani

October 6, 2025

Kwalara ta kashe mutane 4,778 a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024

October 6, 2025

NDLEA ta kama tarin ƙwayoyi da ake shirin safararsu zuwa Birtaniya

October 6, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

By WafsymOctober 20, 2025

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamna daga wani yanki na kudu na ƙasar nan wanda…

Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya

September 27, 2025

Barkewar Cututtuka Uku Sun Tayar da Hankalin Hukumomin Lafiya a Nijeriya ‎

September 27, 2025

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

April 13, 2025
© 2025 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.