Bayan shafe wasu makonni ana fama da zafi mai tsanani, birnin Kano ya sake fuskantar yanayin sanyi mai ƙarfi tare da ƙura da hazo, abin da ke nuna shigowar lokacin hunturu.
Sauyin yanayin ya fara ne a ƙarshen makon da ya gabata, inda mutane da dama suka fara jin tasirinsa a rayuwarsu ta yau da kullum. Wasu mazauna birnin na cewa irin wannan yanayi na nuna yadda sauyin yanayi ke ƙara bayyana a Arewa cikin ‘yan shekarun nan.
Majalisar Dokokin Legas Ta Amince Da Kasafin Kuɗin 2026 Na Naira Tiriliyan 4.4
Wakilinmu ya tattauna da wasu mazauna Kano domin jin ra’ayoyinsu kan yadda wannan yanayi ke shafar kasuwanci, zirga-zirga da lafiyar jama’a.
Rukayya Ibrahim daga Goron Dutse ta ce yanayin bana ya bambanta da na shekarun baya.
“A ganin nawa, hakan na da alaƙa da ƙarancin ruwan sama a bara. Idan ruwan sama ya yi yawa, sanyi yakan fi tsanani,” in ji ta.
Sai dai ta ce wannan yanayi na kawo cikas ga kasuwancinta na sayar da kayan sha masu sanyi.
“Idan sanyi ya yi yawa, mutane ba sa saya. Ni na fi samun riba idan rana na da zafi,” ta ƙara da cewa.
A nata ɓangaren, Hafiz Umar, ɗan kasuwa a Kantin Kwari, ya ce sanyi yana rage zafin kasuwa, amma ƙura na kawo matsala.
“Sanyi yana sauƙaƙa harkokin kasuwa, amma ƙurar hazo na kawo mura da tari, sannan tana iya lalata kaya,” in ji shi.
Wasu mazauna Kano sun ce sun riga sun fara jin tasirin wannan yanayi a lafiyarsu.
Bilkisu Ibrahim daga Sabuwar Gandu ta ce ta kamu da mura da zazzabi sakamakon canjin yanayi.
“Yanzu dole in rika kula sosai, musamman da ruwan da nake amfani da shi,” in ji ta.
A gefe guda kuma, wasu na ganin sanyi a matsayin alheri, musamman ganin watan Ramadan na gabatowa.
Ibrahim Shehu ya ce:
“Idan wannan yanayi ya ci gaba har lokacin azumi, hakan zai rage wahalar zafi.”
Komawar sanyi da hazo a Kano ya jawo ra’ayoyi mabambanta daga jama’a. Yayin da wasu ke jin daɗin sauƙin yanayi, wasu kuma na fuskantar ƙalubale a kasuwanci da lafiya. Masana dai na danganta irin wannan canji da matsalar sauyin yanayi da ke ƙara bayyana a duniya.

