Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta shiga jimami bayan rasuwar mambobinta guda biyu a ranar Laraba.
Hon. Aminu Saad Ungogo, wanda ke wakiltar Ƙaramar Ungogo, shi ne mutum na farko da ya rasu a ranar Laraba.
Labarin rasuwarsa, na cikin wani saƙo da hadimin gwamnan Kano, Ibrahim Adam, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Aminu Saad Ungogo
“Allah Ya gafarta wa Hon. Aminu Saad Ungogo, ɗan Majalisar Jihar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar a Jihar Kano,” in ji Adam.
Sa’o’i ƙadan, aka sake samun labarin rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji, wanda ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni.
Sarki Aliyu Daneji
Shi kuma mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya sanar da rasuwarsa a shafinsa na Facebook.
“Innalillahi Wa Inna Ilaihirrajiun. Hon. Sarki Aliyu Daneji, ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni a Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya rasu yau sa’o’i ƙadan bayan rasuwar takwaransa,” in ji shi.
Kawo yanzu babu cikakken bayani game da rasuwarsu.

